Kungiya ta karrama ’ya’yanta a Kumo
Wata Kungiya da ba ta Gwamnati ba, mai suna Kumo Debelopment Association, tare hadin gwiwar gamayyar wasu kungiyoyi uku da suka hada da New age Initiatibe da Muryar Karkara da Akko Concerns Citizens sun karrama fitattun ’ya’yansu guda 24 da suka yi fice wajen taimaka wa al’umma a bangarorin rayuwa daban-daban. Da yake jawabi wajen […]
Wata Kungiya da ba ta Gwamnati ba, mai suna Kumo Debelopment Association, tare hadin gwiwar gamayyar wasu kungiyoyi uku da suka hada da New age Initiatibe da Muryar Karkara da Akko Concerns Citizens sun karrama fitattun ’ya’yansu guda 24 da suka yi fice wajen taimaka wa al’umma a bangarorin rayuwa daban-daban.
Da yake jawabi wajen ba da lambobin yabo a fadarsa, Mai Martaba Sarkin Akko, Alhaji Umar Muhammad Atiku, taya murna ya yi ga wadanda aka karrama din; inda ya ce yana da kyau a ci gaba da zakulo ’ya’yan yankin da suka yi fice ana karrama su, wanda hakan zai kara wa wasu kwarin gwiwa wajen yin abin kirki.
Sarkin Akkon ya ce wadanda ba su shiga jerin wadanda aka karrama din yanzu ba, ba wai don ba su kai bane, a’a ba zai yiwu a yi komai a lokaci guda ba; amma dai ya ce su kara hakuri zai iso kan su inda ya nemi hadakar kungiyoyin su dinga irin wannan karamcin duk shekara, domin zaburar da wasu su tashi tsaye.
Ya kuma ce wanann karamci da aka yiwa ’ya’yan garin na Kumo shaida ce ta wakilci na gari da suke yi wanda a rayuwa duk abinda mutum yake yi ana kallon sa kuma wata rana zai ga sakayya.
Mai Martaba, ya kara da cewa irin rikice-rikicen da ake samu a tsakanin mabiya addinai da na kungiyoyi yanzu saboda ci gaban da ake samu na wayar da kan al’umma ya ragu sosai kowa yana rungumar kowa a matsayin ’yan uwa.
Daga nan sai Sarkin ya nada wadanda aka karrama din su 24 a matsayin kwamiti da za su yi aiki su fidda wanda zai zama shugaba a tsakaninsu, wajen ciyar da harkar ilimin yankin gaba, domin a cewarsa ya lura akwai wadanda suke fita a makarantu ba tare da sun gama ba da yawa.
Dakta Babayo Ardo, daya ne daga cikin ‘ya’yan yankin da ke da zama a Abuja kuma shi ma ya karbi lambar yabon, ya ce wanann nauyi da Sarki ya dora musu na zama wakilan ilimi sun karbi abin hannu bibiyu, kuma za su yi dukkan mai yiwu wa don ganin sun sauke nauyin da aka dora musu.
Ya ci gaba cewa, zai yi magana da sauran ‘ya’yan garin da ke Abuja don ganin yadda suma za su shigo a dama da su wajen ganin sun bada tasu gudumawar a wannan bangare na ciyar da ilimi gaba domin ilimi shi ne kashin bayan al’umma.
Shi ma Khadi Hadi Aminu Pindiga, da ya samu lambar yabon ya ce shi bai yi tsammani samun wannan lamba ba saboda a tunaninsa irin gudumawar da yake bayarwa ba ta kai a karrama shi ba.
Ya ce a shirye suke da su dauki nauyin da Mai Martaba ya dora musu na wannan kwamitin kula da ilimi domin ai dama aikin al’umma a kansa suke kullum ba sabon abun bane a wajensu.
Da yake tsokaci Shugaban Kungiyar ci gaban garin na Kumo Usman Muhammad Bafeto, cewa ya yi sun shirya wannan taro ne musamman domin karrama ‘ya’yansu da suka bada gudumawa a bangarorin rayuwa daban-daban don karfafawa wasu guiwa suma su gani don su fara idan ma da basa yi.
Ya kuma yi amfani da wannan damar ya godewa Mai Marta Sarkin Akko na yadda ya amince aka gudanar da taron a fadarsa kuma ya ba da tasa gudumawar na Uban Kasa.
Taron ya samu halartar ’ya’yan Akko da ke ciki da waje maza da mata don karawa bikin armashi da kuma nuna farin cikinsu da jin dadi kan wannan taro.