Kungiya ta koya wa matasa da mata 200 sana’o’i a Kaduna
Wata kungiyar matasa da ke Gundunmar Rigasa a Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna ta yaye dalibai mata da maza 200 da ta koya wa sana’o’i domin dogaro da kansu. Daga cikin wadanda aka yaye a makarantar har da wadanda ba Musulmi ba wato mabiya addinin Kirista duk da cewa makarantar tana tsakiyar Musulmi ne. […]
Wata kungiyar matasa da ke Gundunmar Rigasa a Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna ta yaye dalibai mata da maza 200 da ta koya wa sana’o’i domin dogaro da kansu.
Daga cikin wadanda aka yaye a makarantar har da wadanda ba Musulmi ba wato mabiya addinin Kirista duk da cewa makarantar tana tsakiyar Musulmi ne.
Bikin yaye daliban ya gudana ne a harabar makarantar da ke Titin Kwanar Gurguwa a Rigasa, Daraktan Kungiyar, Malam Abdul’aziz Mohammed Madugu Chanchangi ya ce makarantar ba ta nuna bambancin a tsakanin dalibanta.
Ya ce kusan dukkan wadanda aka yaye ’yan Gundumar Rigasa ce da kewaye kuma hakan na nuna cewa akwai bukatar fahimta a tsakanin Musulmin Rigasa da wadanda ba Musulmi ba da ke gefen Rigasa.
Ya ce an koya wa daliban sana’o’i kamar dinki da yin takalma da kwalliya da aski da ilimin kwamfuta sai gyaran wutar lantarki da hada zanen gado na zamani da yin abinci ko girke-girke da sauransu.
“Yanzu haka mun yaye dalibai 200 amma 456 za mu bai wa takardun kammala makarantar. Manufarmu a matsayinmu na matasan wannan yanki na Rigasa shi ne mu ga cewa matasanmu mata da maza sun samu sana’ar yi domin dogaro kansu,” inji shi.
Ya yi kira ga gwamnati ta taimaka wa wadanda aka yaye da jari wanda hakan zai taimaka su rika amfani da abin da suka koya.
Shi ma da yake jawabi a wajen, Malam Hussaini Sani, ya bayyana cewa sana’a na da matukar muhimmanci ga rayuwar matasa domin da sana’a magabata suka rayu.
Don haka sai ya bukaci wadanda aka yaye su tabbatar da cewa sun yi amfani da abin da suka koya domin dogaro da kansu.
Ya shawarci iyaye su rika tura ’ya’yansu inda za su koyi sana’o’i ko da kuwa suna zuwa makaranta domin rashin sana’ar hannu ba daidai ba ne.
Sa’annan ya yaba wa kungiyar matasan da suka kafa wannan cibiyar koyar da sana’o’i tare da yi musu fatan alheri.