Kungiya ta nemi a kara wayar da kan masu zabe

Kungiyar Tsoma Jama’a wajen Tabbatar da Shugabanci Nagari (Organisation for Community Cibil Engagement) ta ce akwai bukatar a kara wayar da kan masu zabe kan yadda za su kada kuri’arsu don guje wa samun yawaitar kuri’u marasa kyau a lokacin zabe. Shugaban Kungiyar Kwamared Abdurrazak Alkali ne ya bayyana haka a yayin da yake tattaunawa […]

Kungiya ta nemi a kara wayar da kan masu zabe
Kungiya ta nemi a kara wayar da kan masu zabe

Kungiyar Tsoma Jama’a wajen Tabbatar da Shugabanci Nagari (Organisation for Community Cibil Engagement) ta ce akwai bukatar a kara wayar da kan masu zabe kan yadda za su kada kuri’arsu don guje wa samun yawaitar kuri’u marasa kyau a lokacin zabe.

Shugaban Kungiyar Kwamared Abdurrazak Alkali ne ya bayyana haka a yayin da yake tattaunawa da manema labarai a Kano, inda ya bayyana cewa a zaben Shugaban Kasa da ya gabata mutane da dama sun yi asarar kuri’unsu sakamakon rashin sanin yadda za su kada kuri’a. “An samu wurare da dama da masu kada kuri’a suka rika yin zabe ba tare da sanin takamaimen yadda ya kamata su yi shi ba, ko wajen nade takardar za ka samu mutane da dama ba su iya ba, wanda muke ganin hakan ya faru ne sakamakon rashin wayar da kan masu zabe,” inji shi.

Ya yi kira ga jam’iyyu su rika wayar wa jama’a kai game da yadda za su kada kuri’arsu a lokutan yakin neman zabe maimakon zantuttukan da ake yi a wannan lokaci. Ya ce “Wayar da kan masu zabe ba aiki ne na Hukumar INEC ita kadai ba, hatta jam’iyyu akwai rawar da za su taka a wannan fanni ta hanyar koya wa jama’a yadda ya kamata su kada kuri’arsu maimakon surutai da ake yi musu wadanda ba su da wani cikakken muhimmanci.”

Kwamared Abdurrazak wanda yana daga cikin masu sanya ido kan yadda zabe ya gudana ya ce duk da cewa an samu nasarar gudanar da zaben, an samu wasu tsaiko sakamakon tutsu da na’urar tantance masu zabe ta yi a wasu wuraren. “Za a iya cewa na’urar tantancewa ta yi aiki kashi hamsin yayin da kashi hamsin kuma aka gudanar da zaben ba tare da amfani da na’urar ba. wato na’urar ta tantance katin masu zabe amma ba ta tantance yatsunsu ba,” inji shi

Ya yaba wa Hukumar INEC game da sabon tsarin da ta fito da shi na tantance masu zabe tare da gudanar da zaben a lokaci guda inda ya ce hakan ya saukaka tare da inganta harkar gudanar da zaben.

Kungiyar ta bayyana jin dadinta game da yadda aka gudanar da zaben da ya gabata cikin kwanciyar hankali da lumana a mafi yawan sassan Jihar Kano.