Kungiya ta nemi hukuma ta binciki faifan bidiyon Ganduje
Wata kungiyar tabbatar da shugabanci nagari ta mika takardar korafi ga Hukumar Karbar Kofare-Korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, a karkashin shugabancin Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, tana neman hukumar ta kaddamar da bincike a kan Gwamnan Jihar, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, bisa zargin da ake yi masa na karbar […]
Wata kungiyar tabbatar da shugabanci nagari ta mika takardar korafi ga Hukumar Karbar Kofare-Korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, a karkashin shugabancin Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, tana neman hukumar ta kaddamar da bincike a kan Gwamnan Jihar, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, bisa zargin da ake yi masa na karbar cin hanci, kamar yadda wani faifan bidiyo ya nuna.
Kungiyar mai suna Concern for Prudent Leadership ta ce ta aike da wasikar ce tana neman a yi bincike don a tabbatar da gaskiya. A cikin takardar korafin mai dauke da sa hannun shugabanta, Mukhtar Sani Mandawari, ta ce duk da cewa Gwamnan yana da rigar kariya; amma hukumar za ta iya gudanar da bincike a kansa don sanar da al’umma gaskiyar lamari a kan wancan faifan bidiyo kamar yadda Hukumar EFCC ta gudanar da makamancin wannan bincike a kan tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose, a lokacin yana kan kujerar Gwamna inda kuma bayan ya sauka ta dora da bincikenta.
Wani jami’i a Hukumar Karbar Korafe-Korafen mai suna Bashir Kabir Rabi’u ya ce tun lokacin da hukumar ta karbi takardar korafin ta mika ta ga Sashen Bincike na Hukumar don fadada bincike.
Majiyar Aminiya ta ce Shugaban Hukumar Barista Muhyi Rimin Gado ya ce hukumarsu tana aiki ne bisa bin dokoki tare da gudanar da aikinta ba tare da jin tsoro ba, a cewarsa wannan ba shi ne karo na farko da hukumar ke gudanar da bincike a kan masu rike da madafun iko a jihar ba.