kungiya ta tallafa wa marayu 90 a Kano
Marayu maza da mata su 90 ne daga kananan hukumomin Gwarzo da Shanono da Kabo da Rimin Gado da Rogo da dambatta da kuma Makoda suka samu horo tare da kayan sana’oi a wani kasaitaccen taro da aka gudanar ranar asabar din da ta gabata. An ba da horo kan sana’ar dinki da daukar hoto […]
Marayu maza da mata su 90 ne daga kananan hukumomin Gwarzo da Shanono da Kabo da Rimin Gado da Rogo da dambatta da kuma Makoda suka samu horo tare da kayan sana’oi a wani kasaitaccen taro da aka gudanar ranar asabar din da ta gabata.
An ba da horo kan sana’ar dinki da daukar hoto da aikin daukar fina-finai da sauran sana’oi na dogaro da kai wadanda za su taimaki wadannan marayu maza da mata ta yadda rayuwar su za ta zamo abar misali a cikin al’umma.
An raba kekunan dinki da na’urar daukar hoto da na bidiyo wato kyamarori da na’urorin da sauran abubuwa na sana’oi ga wadannan marayu 90 bisa la’akari da irin abubuwa da suka koya
Bayan kammala bikin raba kayayyakin, wakilin mu ya sami tattaunawa da wasu daga cikin marayun da suka amfana da tallafin kungiyar, inda Shehu Alkasim Unguwar Tudu daga karamar hukumar Gwarzo ya shaida wa Aminiya cewa zai yi amfani da abin da ya samu wajen dogaro da kai musamman ganin cewa zamani ya canza.
Sannan ya yi kira ga ‘yan uwansa maza da mata da suka samu wannan tallafi da su sani cewa an zabe su ne domin a taimaki rayuwarsu don haka ka da su yi wasa da kayayyakin da aka ba su, sannan kuma ya gode wa wannan kungiya ta SWATCH bisa tausayawar da take wa marayu ba tare da nuna gajiyawa ba.
Ita ma wata wadda ta ci moriyar wannan tallafi mai suna Shamsiyya Mohammed Aliyu daga karamar hukumar dambatta ta nuna jin dadinta na yadda kungiyar take zakulo yara maza da mata tana taimaka musu ganin cewa yanzu ana cikin wani irin yanayi na bukatar samun taimako daga kowane bangare, kana ta yi alkawarin yin amfani da na’urar daukar hoto da aka bata domin ci gaba dasana’ar daukar hoto a lokutan bukukuwan da suka shafi mata.
A nasa bangaren, wakilin hakimin dambatta kuma sarkin bai na Kano Baba Ado Muktar Sarkin Bai ya ce idan ana samun kungiyoyi irin SWATCH a cikin al’uma, ko shakka babu za a ci gaba da kyautata zamantakewar jama’a kamar yadda ake gani a sauran kasashe duniya.
Sannan ya bayyana cewa gundumar dambatta tana godiya matuka bisa wannan tallafi da ta bai wa yaran yankin wadanda kuma suke da bukatar taimako ta kowace fuska, inda kuma ya isar da sakon Sarkin ban Kano Alhaji Muktar Adnan na fatan alheri ga ita wamnan kungiya ta SWATCH wadda take aiki wajen bunkasa rayuwar al’umma ba tare da gajiyawa ba.
Daga karshe, manajan gudanarwa na kungiyar ta SWATCH Malam Umar Muhammad ya bayyana cewa kungiyar za ta ci gaba fa tallafawa marayu maza da mata da kuma yara marasa galihu domin bunkasa rayuwar su kamar yadda manufofin kafata suke.
Ya kuma sanar da cewa za su rika bibiyar dukkanin yaran da suka sami wannan tallafi domin tabbatar da cewa kowa yana gudanar da sana’ar sa kuma sana’ar tana cimma nasar. Sannan ya yi ban gajiya ga dukkanin wadanda suka sami halartar wannan biki.
Kafin wannan taro na bada tallafi, kungiyar ta SWATCH ta yi fice wajen tallafawa kananan yara maza da mata ta fannoni daban-daban wadanda suka hada da kula da lafiya da ilimi da inganta yanayin asibitoci da sauran abubuwa na taimakon al’umma.
Mafiya yawan ayyukan da kungiyar ke yi ne ya sanya take samun gayyata daga manyan kungiyoyi na duniya domin tsarawa da kuma aiwatar da wasu aikace-aikace na ceton al’umma musamman yara kanana marasa galihu da kuma marayu da suke bukatar taimako.