Kungiya ta tallafa wa ’yan Jurun a Legas

Kungiyar da ke kula da jin dadin fursunoni wacce wasu matasan garin Agege suka asassa ta kai ziyara gidan yari na Kirikiri da ke Legas, inda ta bayar da tallafin kayayyakin masarufi ga fursunoni domin ba su damar samun natsuwa da kwarin gwiwar bautar Ubangiji a lokuta masu tsada wato karshen watan azumin Ramadan da […]

Kungiya ta tallafa wa ’yan Jurun a Legas

‘Yan qugiyar a lokacin ziyarar su a gidan kaso na kirikiri Legas

Kungiyar da ke kula da jin dadin fursunoni wacce wasu matasan garin Agege suka asassa ta kai ziyara gidan yari na Kirikiri da ke Legas, inda ta bayar da tallafin kayayyakin masarufi ga fursunoni domin ba su damar samun natsuwa da kwarin gwiwar bautar Ubangiji a lokuta masu tsada wato karshen watan azumin Ramadan da ma yin bukukuwan Sallah karama cikin walwala.

shugaban kungiyar wanda ya jagoranci rangadi zuwa gidan kason na kirikiri da ke Legas Malam Idris Usman Dan Innah ya shaidawa Aminiya cewa, sun ziyarci fursunonin ne domin basu kwarin guiwa inda suka basu kayayyakin tallafi da suka hadar da na abinci da kayayyakin sawa da sabulan wanka da manshafawa da na wanke baki da dai sauran su, ”Kuma a wannan karon mun taho da samarin mu da dattijawan mu da yara matsakaita kusan mutum 70 daga garin Agege domin su shiga gidan kaso su gani da idanun su saboda su dau izina su sani cewa, ’yancin walwala da suke da shi abu ne muhimmmi, domin a kyale ka kana walwala abin ka, ka je inda kake so a lokacin da ka so wani muhinmmin abu ne baya ga lafiyar da Allah ya baka, zuwan da mu kayi fursunonin murna suke tayi domin mun kawo masu ziyara mun kuma dan sami wani abu mun basu, kaga wannan zai faranta masu su kuma mutanen da muka zo dasu musanmman ma matasa za su dai izina za su guji aikata laifin da zai kai su gidan kaso domin sun je sun gani sun shaida da idanun su.“ In ji shi.

Dakta Kasim Garba Kurfi yana daya daga cikin wadanda suka ziyarci gidan kason ya shaidawa Aminiya cewa, sama da shekaru 18 suka yi suna ziyartar ‘yan gidan yarin domin tallafa masu da matsalolin su, ”Mu da su mun zama daya, suna kiran mu a waya duk sanda suke bukatar taimakon mu na gaggawa, idan an sami wani ya rasu a cikin su suna kiran mu muje mu yi wa mamacin sutura mu binne shi kamar yadda yake a addinin musulumci, wadanda aka sako sukan neme mu mu basu tallafi wasu mu mayar da su garuruwan su na asali, mun riga mun shaku da su sama da shekaru 18 kuma duk mako sai mun ziyarce su, abin ya zame mana jiki, sabo ni a kusa nake da su“. In ji shi.

Alhaji Sani Muhammad Baba daya ne daga cikin matasa ’yan kungiyar ya shaidawa Aminiya cewa, sun asassa kungiyar tallafawa ’yan fusunan tare da sauran mabukata, a baya kungiyar baya da rijista amma yanzu mun yi mata rijista kuma muna neman taimako ne a tsakaninmu mu ’yan kungiyar ta yadda kowa ke bada tasa gudunmawar domin tallafa masu kuma muna kokrin fadada wannan izuwa ga duk masu bukatar tallafawa domin suma su shiga aikin ladan, domin bai kamata a ce an barwa gwamnati ita kadai alhakin kulawa da jin dadin daurarru ba muma zamu iya bada tamu gudunmawar.

Wakilin Aminiya na daya daga cikin wadanda aka kai ziyarar gidan kason dasu, ya zanta da wasu daga cikin wadanda ke tsare a gidan yarin matsakaici na Kirikiri inda ya zanta da wani matashin mai karamin shekaru mai suna Ibrahim, ya ce an kawo shi gidan yarin din sakamakon fdan da yayi da wani mutum da ya buge shi da murfin kofar mota, ”Ina cikin motar zan bude kofa sai na buge shi nan da nan ya kama ni da fada sai budurwar shi ta dau kwalba ta jimin rauni a hannu ganin haka na bangajeta ta fadi sai kwalbar tayi mata rauni a kafada, da ’yan sanda suka kama ni sai da ya na yi mako uku a daure a wajen su ba tare da iyaye na sun san inda nake ba domin sun kira bari na na sanarwa iyaye na inda nake, wani lauya ne da yazo ya ganni ya kira su a waya, yau wata na 11 a nan gidan yarin a daure, muna fita shari’a a kotun da ke gidan yarin amma sau tari lauyan da ta ke kare ni ba ta zuwa tace aiki ya yi mata yawa, a Unguwar Apapa a Legas muke zaune da iyaye na, yau kimanin wata biyar ke nan rabon da iyaye na su ziyarce ni,  matsalar kudi ce tasa har yanzu ba a sallame ni ba, domin da zamu sami taimakon dubu 20 da an sallame ni, wata  yaya ta ta baiwa wanda muka yi fadan da shi Naira dubu 15 amma ya ce, sun yi kadan sai an kara masa domin sun biya kudin jinya na magani wai kuma na fasa masa wayar salular sa, idan aka ba shi kudin zai yarda a janye maganar ayi sulhu“. In ji shi.

Ya ce, babbar matsalar da suke fuskanta a gidan kason shi ne rashin abinci, a wani lokacin abin da aka baka yau zaka raba biyu ka aje rabi domin kaci gobe, sau tari abincin da ake bamu da safe wake ne mai tsakuwa sai mun wanke shi da ruwa kafin mu iya ci, da daddare ko da rana kuma a bamu gari, a zaman da nayi zuwa yanzu ba a taba bamu nama a abinci ba, sai dai irin abincin da wasu kungiyoyi kan kawo mana lokaci zuwa lokaci“. In ji shi.