kungiya ta yi tir da kama mahaifin dalibin da ake zargin ’yan sanda da kisansa

Gamayyyar kungiyoyin masu zaman kansu ta yi tir da kamun da rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta yi wa Alhaji Abdullahi Alfa, mahaifin marigayi Hassan Abdullahi Alfa, dalibi a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, wanda ake zargin ’yan sanda da kashe shi a watan jiya.A cikin wata takarda da Shugaban kungiyar, Malam Nura […]

kungiya ta yi tir da kama mahaifin dalibin da ake zargin ’yan sanda da kisansa
kungiya ta yi tir da kama mahaifin dalibin da ake zargin ’yan sanda da kisansa

Gamayyyar kungiyoyin masu zaman kansu ta yi tir da kamun da rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta yi wa Alhaji Abdullahi Alfa, mahaifin marigayi Hassan Abdullahi Alfa, dalibi a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, wanda ake zargin ’yan sanda da kashe shi a watan jiya.
A cikin wata takarda da Shugaban kungiyar, Malam Nura Iro Ma’aji ya sa wa hannu, kungiyar tana kallon kamun a matsayin wata barazana da tsoratarwa ga iyalin marigayin game da kokarin da suke yi wajen bin hakkin jinin dansu.
“Muna sanar da rundunar ’yan sanda cewa idanunmu na kan duk abubuwan da ke faruwa, ba za mu  gajiya ba wajen sanar da dukkanin kungiyoyin kare hakkin bil’adama na gida Najeriya da na kasashen waje game da lamarin”. Inji takardar.
Har ila yau kungiyar ta yi kira ga rundunar, ba tare da bata lokaci ba, ta bar hanyar yin barazana da kuma tsoratarwa ga iyalin mamacin, musamamn ma mahaifinsa, a maimakon haka, ta bi hanyar da ta dace wajen tabbatar da adalci da gaskiya cikin al’amarin.
Idan za a iya tunawa, a karshen watan jiya ne iyalin Alhaji Abdullahi Alfa suka zargi rundunar ’yan sandan Jihar Kano da kisan dansu Hassan Abdullahi Alfa, sakamakon dandana kudarsa da ya yi a hannun ’yan sandan lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa.
Yayin da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya bayyana cewa rundunar tasu ta kame Alhaji Abdullahi Alfa ne saboda laifin kin cika alkawarin yarjejeniyar da rundunar ta yi da shi a lokacin da ta ba shi belin wasu wadanda ake zargi da aikata wani laifi, inda ya ki ya mayar da masu laifin bayan cikar wa’adin da aka diba masa.
ASP Magaji Majiya ya kara da cewa tuni ma rundunar ta gurfanar da shi a gaban kotu.