Kungiya ta yi wa jarirai 3m alluarar riga-kafi a Arewa
Wata kungiyar mai zaman kanta ta ce aƙalla jarirari miliyan uku a yankin Arewacin Najeriya ta ɗauki nauyin yi wa allurorin riga-kafi. Mubarak Bawa, Shugaban kula da shirin ƙungiyar mai suna New Incentivem ya bayyana cewa sun kirkiri sabon shiri mai taken ‘Da Na Kowa Ne’ domin tallafa wa iyaye da asibitocin gwamnati wajen yi […]
Wata kungiyar mai zaman kanta ta ce aƙalla jarirari miliyan uku a yankin Arewacin Najeriya ta ɗauki nauyin yi wa allurorin riga-kafi.
Mubarak Bawa, Shugaban kula da shirin ƙungiyar mai suna New Incentivem ya bayyana cewa sun kirkiri sabon shiri mai taken ‘Da Na Kowa Ne’ domin tallafa wa iyaye da asibitocin gwamnati wajen yi wa jarirai miliyan uku riga-kafi.
Bawa ya ce daga fara shirin zuwa yanzu, an samu ci gaba sosai wajen yawaitar yaran da ke karbar alluarar riga-kafin, da kuma raguwar mace-macen kananan yara.
“An dabbaka wannan shirin ne a jihohi tara, a kauyuka 4,800 a Najeriya, inda yara fiye da miliyan uku suka ci gajiyarsa.
“Shirin ya bayar da gudummawa wajen rage mace-macen kananan yara musamman ma a Kano, inda muke aiki da fiye da kashi 90 na asibitocin gwamnati domin tabbatar da mun isa ga jariran da ke kananan hukumomin jihar 44.
“Ya zuwa yanzu, yara fiye da 520,000 ne a jihar suka ci gajiyar shirin.
“Haka kuma muna wayar da kan al’umma a duk inda muka ga an samu karancin zuwa karbar riga-kafin daga bayanan da muka tattaro, saboda rage samun jarirai masu nakasa ko marasa lafiya.”
A nasa bangaren manajan shirin Abdul’azeez Abdullahi, cewa ya yi, ƙungiyar za ta ci gaba da ƙarfafa guiwar al’umma da kuma kyautata wa abokan huldarsu da ke faɗin ƙasar nan, bisa kokarin da suke yi wajen ganin shirin ya yi nasara.
“Bayanai na nuna cewa kyautatawa masu yi maka hidima na kara musu kaimi wajen sadaukarwa da kuma jajricewa.
Kuma a karshe zai inganta naka aikin da dama shi ne babban burinmu.