kungiya za ta raba wa dalibai littattafan rubutu a Kaduna
kungiyar dalibai ta Hayin Banki, (HABSU) ta shirya domin fara rab awa daliban firamare da ke Unguwar Hayin Banki a karamar Hukumar Kaduna ta Arewa a Jihar Kaduna littattafan rubutu. Mukaddashin Sakataren kungiyar, Malam Abdullahi Idris ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya. Malam Abdullahi ya ce, sun shirya wannan muhimmin […]
kungiyar dalibai ta Hayin Banki, (HABSU) ta shirya domin fara rab awa daliban firamare da ke Unguwar Hayin Banki a karamar Hukumar Kaduna ta Arewa a Jihar Kaduna littattafan rubutu.
Mukaddashin Sakataren kungiyar, Malam Abdullahi Idris ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya.
Malam Abdullahi ya ce, sun shirya wannan muhimmin aiki ne domin tallafa wa shirin gwamnati na inganta ilimi a jihar, “Kasancewar yanzu karatu a firamare kyauta ne a Jihar Kaduna, shi ya sa muka ce bari mu bayar ta wata gudunmawa ta wata hanyar. Shi ya sa bayan mun tattauna a kan me za mu iya, sai muka amince mu raba littattafan rubutu,” inji shi.
Ya ce “Da yake babban makasudin kafa kungiyar HABSU shi ne inganta ilimi da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a unguwarmu, za mu ci gaba da tallafa wa duk mutanen unguwar da kasa baki daya ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba.”
Game da hanyar samun kudin shiga domin gudanar da harkokin kungiyar, Malam Abdullahi ya ce, “Mu muke karo-karo don gudanar da harkokin kungiyar. Ka ga kamar wannan batu na raba littattafan rubutu, mu muka saya da kudinmu, sai kuma wadansu masu sha’awar taimakon unguwar da suka tallafa. Ba mu yarda mun saka siyasa a cikin lamarin ba, kuma muna taka tsan-tsan da hakan. Amma dai wadansu mutane suna kokari tallafa wa kungiyar gaskiya. Sai dai matsalar watakila ita ce kasancewar ba ma karbar gudunmawar kudi, kawai idan za mu gudanar da wani aiki ko shiri, mukan nemi tallafin kayan aiki ne daga mutane,” inji shi.
Malam Abdullahi ya ce kofarsu a bude take ga duk wanda yake da sha’awar bayar da tallafin littafin a ciki ko wajen unguwar, koda kuwa guda daya ne, domin a cewarsa duk wanda aka taimaka ya yi karatu, to shi ma nan gaba zai taimaki wani.