kungiya za ta samar da karamin banki a Filato
kungiyar Bunkasa Birnin Jos da a Turance ake kira Make Jos Great Again Forum (MJGAF) ta bayyana cewa a yanzu haka tana ci gaba da shirye-shiryen wajen kafa karamin bankin da zai tamaka wa kananan ’yan kasuwa da masu kananan sana’o’i a Jihar Filato. Shugaban kungiyar, Cif Samuila Danko Makama ne ya bayyana haka a […]

kungiyar Bunkasa Birnin Jos da a Turance ake kira Make Jos Great Again Forum (MJGAF) ta bayyana cewa a yanzu haka tana ci gaba da shirye-shiryen wajen kafa karamin bankin da zai tamaka wa kananan ’yan kasuwa da masu kananan sana’o’i a Jihar Filato.
Shugaban kungiyar, Cif Samuila Danko Makama ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi yayin kaddamar kwamitocin kungiyar a sakateriyarta da ke Jos a ranar Asabar da ta gabata.
Ya ce, kungiyar wadda take kunshe da mazauna birnin Jos tun kafin da kuma bayan shekarar 1960 zuwa yau, ta samu kwarin gwiwar samar da bankin ne sakamakon manufofinta na ganin birnin Jos ya bunkasa, inda kuma kananan ’yan kasuwa za su samu fa’ida mai yawa daga bankin.
Cif Makama ya ce kungiyarsu za ta jajirce wajen ganin ta bunkasa birnin Jos ta hanyar amfani da ingantattun hanyoyin da kwalliyarsu za ta biya kudin sabulu wajen ganin birnin ya samu ci gaba mai dorewa.
“Wannan banki da za mu samar zai bai wa kowa damar amfana da shi, babu bambancin addini ko kabila ko yankin da mutum ya fito, kuma mun fito da batunsa ne cike da gaskiya ba wai kumbiya kumbiya ba,” inji shi.
kungiyar ta kuma bukaci matasa su tashi tsaye wajen kama sana’o’i, sannan su guji shaye-shaye hade da tayar da rikice-rikice.