Kungiya za ta yi bikin cika shekara 8

Kungiyar Musulmin Barikin Soji na NDA Kaduna (MYARC) za ta shirya bikin cika shekara biyar da kafuwa. Da yake jawabi ga wakilin Aminiya a Kaduna a kan makasudin shirya wannan biki, Shugaban kungiyar, Malam Abdul’azeez Muhammad Sai’du Afaka ya ce sun kuduri aniyar yin bikin ne domin yin waiwaye da yi wa Allah godiya bisa […]

Kungiya za ta yi bikin cika shekara 8
Kungiya za ta yi bikin cika shekara 8

Kungiyar Musulmin Barikin Soji na NDA Kaduna (MYARC) za ta shirya bikin cika shekara biyar da kafuwa.

Da yake jawabi ga wakilin Aminiya a Kaduna a kan makasudin shirya wannan biki, Shugaban kungiyar, Malam Abdul’azeez Muhammad Sai’du Afaka ya ce sun kuduri aniyar yin bikin ne domin yin waiwaye da yi wa Allah godiya bisa nasarorin da suka samu a wadannan shekaru, kuma za su karrama wadanda suka ba kungiyar gudunmawa ta hanyoyi da da dama.

“Kasancewar mun dade muna gudanar da ayyuka da dama musamman a Barikin NDA na Kaduna, mun samu nasarori da yawa da ba za a iya kiyastwa ba. Ashe ke nan ya kamata mu gode wa Allah bisa taimakonmu da Yake yi tun kafa kungiyar zuwa yanzu. Sannan za mu yi amfani da wannan dama wajen sake fasalin kungiyar domin ta ci gaba da ayyukanta,” in ji shi.

Da ya juya kan dalilin da ya sa suka kafa kungiyar tun asali, Malam Abdul’azeez wanda aka fi sani da Amir ya ce sun kafa kungiyar ce domin su taimaka wa Musulmi mazauna barikin tare da tunatar da su hakkin addini da ke kansu, “Kasancewar rayuwa a bariki sai a hankali kamar yadda wadansu suke cewa, shi ne muka kafa wannan kungiya domin mu isar da sakon Allah a cikin barikin. Muna shirya tarurrukan bita da wa’azuzzuka da gasa daban- daban domin jawo hankalin ’yan uwa Musulmi saboda kada su shagala. Kuma gaskiya cikin ikon Allah da kuma taimakon wadansu daga cikin sojojin da kuma iyaye mata, muna samun nasara sosai. Muna godiya ga Allah,” inji shi.