Kungiyar ADSI ta raba wa matasa 115 tallafin sana’o’i
Kungiyar Ci gaban Arewa ta ADSI reshen Jihar Kano ta raba kayan tallafin sana’o’i ga matasa 115 wadanda ta horar da su a kan sana’o’i daban-daban. Matasan maza da mata sun koyi sana’o’in da suka hada da yadda ake hada tauraron dan Adam da dinki da sarrafa shara da kwalliyar mata da girke-girke da kwarewa […]
Kungiyar Ci gaban Arewa ta ADSI reshen Jihar Kano ta raba kayan tallafin sana’o’i ga matasa 115 wadanda ta horar da su a kan sana’o’i daban-daban.
Matasan maza da mata sun koyi sana’o’in da suka hada da yadda ake hada tauraron dan Adam da dinki da sarrafa shara da kwalliyar mata da girke-girke da kwarewa kan hanyoyin sadarwa na zamani da sauransu.
Shugabar Kungiyar ADSI ta Kasa, Hajiya Khuraira Musa ta bayyana cewa ta kafa kungiyar ce don kokarin dawo da nagartattun dabi’u da aka san Arewa da su wadanda suke kokarin bacewa, tare da magance matsalolin da ke ci wa yankin tuwo a kwarya. “Mun yi tunanin yadda za mu ga Arewa ta dawo kamar yadda aka san ta a baya, sai muka fahimci cewa burinmu ba zai cika ba sai mun magance matsalolin da suke damunmu irin su shaye-shayen miyagun kwayoyi da rashin aikin yi a tsakanin matasanmu,” inji ta.
Hajiya Khuraira ta yi kira ga masu kishin Arewa su koyi dabi’ar tallafa wa yankin ta hanyar sanya Naira dubu biyu a asusun kungiyar duk wata “Abin da muke yi shi ne muna sanya Naira dubu biyu a asusun wannan kungiya duk wata. Ga shi a yanzu mun fara amfani da kudin wajen tallafa wa matasanmu. Muna kira ga sauran ’yan Arewa, Musulmi da Kirista a dukkan sassan kasar nan, su zo mu hadu mu ceto wannan yankin namu. Kofarmu a bude take ga kowa wanda duk ya yarda Arewa tana gabansa ya zo mu yi wannan tafiya tare. Naira dubu biyu muke nema duk wata. Muna da wakilai a dukkan jihohin Arewa. Kuma ayyukanmu za su rika zagayawa a yankunan Arewar,” inji ta.
A jawabin Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi II ya bayyana muhimmancin da ke akwai cikin hadin kan al’umma don taimakon kansu, inda ya ce babu wata kasa da za ta ci gaba a duniya ba tare da al’ummata ta taimaka wa kanta ba.
A cewar Sarkin idan har ana so martabar yankin Arewa ta dawo to dole ’yan Arewa da kansu sun tashi sun yi gyara da kansu maimakon jiran wasu kasashe su zo su tallafa. “Ya kamata ’yan Arewa mu fahimci cewa babu wani da zai zo ya gyara mana yankinmu sai mu kanmu. Domin matsalar da muka samu kanmu a ciki ba wani ba ne ya janyo mana illa mu da kanmu. Matsalolin talauci da shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa da sauransu matsaloli ne da za mu iya gyarawa da kanmu. Kuma wannan gyara ba zai yiwu ba sai kowa ya tashi ya bayar da gudunmawa daidai karfinsa ta hanyar taimakon kai-da-kai tare da neman na kanmu. Gwamnati ita kadai ba za ta iya ba, don haka kalubale ne a agre mu,” inji Sarkin.
Ya bayyana bukatar da ke akwai wajen kafa kananan masana’antu a tsakanin al’umma inda jama’a za samu guraben ayyukan yi ba tare da jiran gwamnati ta samar da aikin yi ba, don haka ya yi kira ga matasan da suka samu tallafin su yi kokari wajen yin aiki da abin da suka koya domin tsayawa da kafafuwansu tare da daukar wadansu mutanen a karkashinsu.