kungiyar Afenifere ta yi watsi da ikirarin shugabannin Fulani
kungiyar Yarabawa Zalla (Afenifere) ta yi watsi da karyata zargin da shuagabannin Fulani suka yi, na cewa Fulani makiyaya ba su da hannu a garkuwar da aka yi da Cif Olu Falaye.Sanata Femi Okunroumi ne ya shaida wa Aminiya haka, ya kara da cewa dalilansu na alakanta Fulanin da garkuwar shi ne, tun a baya […]
kungiyar Yarabawa Zalla (Afenifere) ta yi watsi da karyata zargin da shuagabannin Fulani suka yi, na cewa Fulani makiyaya ba su da hannu a garkuwar da aka yi da Cif Olu Falaye.
Sanata Femi Okunroumi ne ya shaida wa Aminiya haka, ya kara da cewa dalilansu na alakanta Fulanin da garkuwar shi ne, tun a baya akwai takun saka a tsakaninsu da Falaye kuma shi da kansa ne ya fada cewa su ne suka yi garkuwa da shi.
Sanatan, wanda shi ne shugaban kwamitin mai ba tsohon Shugaban kasa Jonathan shawara a kan taron kasa da ya gabata, ya yi kira ga gwamnatin jihohi da su sama wa Fulani makiyaya wuraren kiwo, domin a cewarsa hakan shi zai kawo karshen rigingimun da ke barkewa a tsakanin Fulani makiyaya da manoma kuma hakan shi ne zai ba ’yayan Fulanin damar samun nagartaccen ilimi, ya kuma bunkasa albarkatun dabobbinsu, ya kuma rage wahalhalun da suke sha na tafiye-tafiye, wanda hakan ke jefa su cikin hadurra irin na masu satar shanun da suke kasha su, su kore musu shanu.
Ya kara da cewa su Yarabawa mutane ne masu maraba da baki kuma ba su da matsala da ’yan Arewa, sai dai wasu daga cikin Fulani makiyayan da harkokinsu ke barazana da zaman lafiyar yankin. Ya kuma kara da cewa kofar kungiyar a bude take da su tattauna da shugabannin Fulannin, domin a cin ma matsaya.
Shugaban kungiyar Mayyati Allah a jihohi 6 na Kudu maso yamma, Alhaji Kabiru Muhammad Labar, ya shaida wa Aminiya cewa taron da suka yi a karshen makon jiya, sun yi ne domin su kwantar wa jama’arsu hankali tare da samun mafita, su kuma karyata zargi da neman bata masu suna da wasu ke kokarin yi. Ya kuma ce kwalliya ta biya kudin sabulu, domin har a wajen kasar nan ake kiran su ana jinjina masu a kan matakan da suka dauka na kare mutuncin Fulani makiyaya.
Ya kuma ce kofarsu a bude take ga duk wanda zai neme su a tattauna, ya kuma jaddada cewa doka ce ta ba su damar shiga ko’ina ne a Afirika ta yamma, domin su yi kiwon dabobbinsu. Ya yi kira ga gwamnati da ta tallafa wa bangaren na kiwon dabobbi domin a cewarsa, ta haka ne za a magance fitintinun da ke tasowa. Ya kuma yi kira ga Fulani makiyaya da su ba ilimi fifiko, domin zamani ya canza komai sai da ilimi don haka ya zama wajibi su dinga tura ’ya’yansu makaranta don neman ilimi.