kungiyar agaji ta Munazzamatul Islam ta kara kaimi a Kalaba

kungiyar agaji ta Munazzamatul Islam ta Jihar Kurosriba ta ce ta dukufa wajen sanya ido tare da daukar kwakkwaran mataki na kawar da bata gari da kuma dukkanin nau’in ta’addanci, musamman lura da yadda kasar nan ta tsinci kanta, lamarin da ke bukatar matsananciyar addu’a da jajircewa.Haka nan kuma daga lokacin da ta kungiyar, ta […]

kungiyar agaji ta Munazzamatul Islam ta kara kaimi a Kalaba
kungiyar agaji ta Munazzamatul Islam ta kara kaimi a Kalaba

kungiyar agaji ta Munazzamatul Islam ta Jihar Kurosriba ta ce ta dukufa wajen sanya ido tare da daukar kwakkwaran mataki na kawar da bata gari da kuma dukkanin nau’in ta’addanci, musamman lura da yadda kasar nan ta tsinci kanta, lamarin da ke bukatar matsananciyar addu’a da jajircewa.
Haka nan kuma daga lokacin da ta kungiyar, ta dukufa wajen mayar da hanakali kan tsaro da kuma kariya, idan ban da wani mutum daya da ta ce ta cafke da ya zo daga Fatakwal, ya ce masu shi ma dan agaji ne na Munazzamatul Islam a Fatakwal a sakamakon tsananta bincike da suka yi ai suka gano ashe cewa makaryaci ne, yana ci ne da ceto ne kurum da sunan kungiyar agajin.
“Ya ce mana shi dan agajinmu ne a Fatakwal, ya zo da kayan aikin agaji irin namu. To a sakamakon bincike da muka tsananta ne sai muka gano ko a can ma Fatakwal din ba dan agaji ba ne amma ya fake da sunan kungiyar agaji ne yana sayar da kayan agaji. Tuni kuma muka dauki mataki don hana afkuwar na gaba.” Kamar yadda Alhaji Musa Yunusa, Sakataren kungiyar Agaji ta Munazzamatul Islam da ke Kurosriba ya shaida wa Aminiya, jim kadan da kammala taron bita na ’ya’yan kungiyar da ke kananan hukumomin birnin Kalaba da kuma Kalaba ta kudu, da aka gudanar a Kalaba hedkwatar jihar.
Ya ci gaba da cewa saboda abubuwan da ke faruwa a kasa ne uwar kungiyar ta kasa ta bullo masu da wasu dabaru da za su rika gane cikakkken dan kungiyar agaji ta Munazzamatul Islam da kuma na jabu da ke son fakewa da kayansu yayi ta’addaci.
 A saboda haka ne ma ya kara da cewa: “Muka dauki matakin wadata ilahirin masallatanmu da na’urar tantace mutum. Sai an tantance shi, ba sani ba sabo kafin mutum a bar shi ya shiga masallaci da kuma sauran matakan tsaro da sirrin mu ne; ba za a iya fada ba.”