kungiyar al-kaeda ta dauki alhakin kai harin gidan mujallar Faransa
Manyan Shugabannin al-kaeda reshen kasar Yemen ya dauki alhakin harin da aka kaiwa mujallar barkwancin nan ta Charlie Hebdo da ke kasar Faransa, inda aka kashe mutum 12 ofishinta a makon jiya. Babban Kwamandan kungiyar Nasr al-Ansi ya bayyana a wani faifan bidiyo mai tsawon minti 10, wanda aka sanya a intanet shekaranjiya Laraba, inda […]
Manyan Shugabannin al-kaeda reshen kasar Yemen ya dauki alhakin harin da aka kaiwa mujallar barkwancin nan ta Charlie Hebdo da ke kasar Faransa, inda aka kashe mutum 12 ofishinta a makon jiya.
Babban Kwamandan kungiyar Nasr al-Ansi ya bayyana a wani faifan bidiyo mai tsawon minti 10, wanda aka sanya a intanet shekaranjiya Laraba, inda ya ce kisan kiyashin Charlie Hebdo da aka yi daukar fansa ne daga cin mutumcin Manzon Allah (SAW). Kwamandan ya bayyana kasar Faransa da shedaniya da kuma shan alwashin kai wasu sabbin hare-hare a kasar. Ya ce reshen kungiyar shi ne ya tsara da kuma daukar nauyin harin da aka kaiwa mujallar a makon jiya.
’Yan bindiga sun kai hari kamfanin mujallar ne bayan ta wallafa wani zane da ke takalar mabiya addinin Musulunci, inda editanta da kuma hudu daga cikin masu zanenta da ’yan sanda biyu suka rasa rayukansu. Mujallar ta yi suna wajen wallafa zanen batanci ga Manzon Allah a baya.
An kafa kungiyar al-kaeda reshen Yemen ne a watan Janairun shekarar 2009. Kuma kasar Amurka na bayyana reshen da wanda ya fi kowanne hadari, wannan ya kasar sa take kaiwa shugabannin kungiyar hari ta sama da jirage marasa matuka.