Kungiyar Alarammomi a binciki shirin tsoma boko a makarantun allo na Kano
Kungiyar Matasan Alarammomi ta Kasa ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano ta binciki yadda shirin koyar da almajirai ilimin boko ke gudana a jihar. Shugaban Kungiyar, Alaramma Bayero Badamasi Muhammad ne ya yi wannan kira lokacin da yake tattunawa da Aminiya a Kano, inda ya bayyana sabon shirin a matsayin wani abu na ci […]
Kungiyar Matasan Alarammomi ta Kasa ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano ta binciki yadda shirin koyar da almajirai ilimin boko ke gudana a jihar.
Shugaban Kungiyar, Alaramma Bayero Badamasi Muhammad ne ya yi wannan kira lokacin da yake tattunawa da Aminiya a Kano, inda ya bayyana sabon shirin a matsayin wani abu na ci gaba gare su; sai dai a cewarsa, akwai kura-kurai a ciki inda ya ce an siyasantar da shirin. “Babu shakka shirin abin ayaba wa gwamnati ne, domin ci gaba ne gare mu. Duk da cewa tuni muka karbi ilimin boko. Domin da girmanmu muka shiga makarantun ilimin manya don mu yaki jahilci wanda a yanzu har mun kammla rubuta jarrabawar sakandare kuma muna da burin ci gaba da karatu,” inji Alaramma Bayero.
Sai dai ya nemi a yi wa tsarin kwaskwarima: “Yadda ake gudanar da shirin akwai bukatar gwamnati ta duba lamarin, saboda yadda aka bar shi a hannun ’yan siyasa suna cin karensu ba babbaka. Makarantu da dama da suka cancanta su shiga cikin tsarin ba a sanya su ba saboda bambancin siyasa,” inji shi.
A cewar Alaramman, “Idan ana so a samu biyan bukata a rayuwa kowane abu ana bayar da shi ga wanda fanninsa ne. Babu yadda za a dauko dan siyasa a ba shi harkar gudanar da sha’anin makarantun Tsangaya a samu abin da ake so.”
Alaramma Bayero, ya ce makarantun da gwamnatin ta diba a matakin gwaji, abu ne da ba za a iya samun sakamako mai kyau ba. “Idan kin duba gwamnati ta ce za ta fara da tsangaya 1,500. A gaskiya sun yi yawa, lura da abubuwan da gwamnatin ta ambata tana so ta samar na tafiyar da karatun kamar ciyar da daliban tare da ba alarammomin tsangaya kudin gudanarwa, wannan abu ne mai yawa. Kamata ya yi a rika dibar makarantun kadan-kadan a hankali za a samu a kai ga nasarar da ake bukata.”
Malamin ya kara da cewa akwai bukatar gwamnati ta samar da wani kwamiti mai karfi ko wani tsari da zai rika bibiyar gaba dayan shirin “A kwanakin baya sai ga wani malami daya daga cikin malaman da gwamnati ta dauka ya zo makarantarmu, yana tambayar wata tsangaya da aka tura shi ya koyar, amma da na bincike shi, sai na gano cewa babu wata shaida da aka ba shi da take nuni da cewa malami ne,” inji shi.