kungiyar alarammomi ta bukaci gwamnatin Kano ta cika alkawari
kungiyar Alarammomi ta Jihar Kano wato Hisburrahman Fi Tilawatil kur’an ta nemi gwamnatin Jihar Kano ta cika alkawarin da ta yi mata na inganta harkar almajirci a jihar.Shugaban kungiyar, Alaramma Tukur Ladan ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Kano a karkashin Rabi’u Musa Kwankwaso ta ce za ta samar wa kungiyar wurin karatu na din-din-din da […]
kungiyar Alarammomi ta Jihar Kano wato Hisburrahman Fi Tilawatil kur’an ta nemi gwamnatin Jihar Kano ta cika alkawarin da ta yi mata na inganta harkar almajirci a jihar.
Shugaban kungiyar, Alaramma Tukur Ladan ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Kano a karkashin Rabi’u Musa Kwankwaso ta ce za ta samar wa kungiyar wurin karatu na din-din-din da wurin gudanar da sana’o’i kamar su kanikanci da dai sauransu.
Ya ce: “Da farko gwamnatin ta yi kamar da gaske take, inda a shekarar 2011 ta umarci mu kafa wani kwamiti da zai taimaka wajen ba da shawarwari don ganin an inganta harkar almajiranci a jihar. Haka kuma a shekerar 2012, gwamnatin ta raba wa almajirai fom kamar da gaske. To amma shiru ka ke ji kamar an shuka dusa.”
Ya ci gaba da cewa mafi yawan masu sana’o’i a jihar ta Kano sun samu tallafin gwamnatin amma fa ban da su, “Sau da yawa muna ji ana taimaka wa mutane a Jihar, misali bayan mata da matasa, an taimaka wa wasu masu sana’o’i a jihar kamar su wanzamai da mahauta. A baya-bayan nan an yi wa matasa ‘yan kwallon kafa goma ta arziki da dai sauransu. Mu kuwa mahaddatan al-kur’ani har yanzu babu wani agaji da aka yi mana” Inji Alaramman.
Duk da haka, ya bayyana goyon bayan kungiyarsu ga gwamnatin jihar , tare da fatan Allah Ya ba ta ikon cika alkawuran da ta dauka.