kungiyar Alarammomin Jihar Gombe ta karrama Gwamna dankwambo

kungiyar Alarammomi Mahaddata Alkur’ani ta Jihar Gombe ta karrama Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo bisa yadda yake ba su kulawa.Da yake yiwa Aminiya karin haske jim kadan bayan kammala taron karramawar, Shugaban kungiyar Alarammomin ta Jihar, Alaramma Muhammad Sadisu Mai Babban Allo, ya ce sun karrama Gwamnan ne saboda irin kulawar da yake ba […]

kungiyar Alarammomin Jihar Gombe ta karrama Gwamna dankwambo
kungiyar Alarammomin Jihar Gombe ta karrama Gwamna dankwambo

kungiyar Alarammomi Mahaddata Alkur’ani ta Jihar Gombe ta karrama Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo bisa yadda yake ba su kulawa.
Da yake yiwa Aminiya karin haske jim kadan bayan kammala taron karramawar, Shugaban kungiyar Alarammomin ta Jihar, Alaramma Muhammad Sadisu Mai Babban Allo, ya ce sun karrama Gwamnan ne saboda irin kulawar da yake ba su a matsayinsu na kungiya wadda a baya ba sa samun haka.
Ya ce gwamnati ta saba bai wa kungiyoyi tallafi idan watan azumi ya kama wanda su ba a ba su, amma daga hawan Gwamna dankwambo mulki su ma ya sa su a ciki inda ake ba su. Hakan ne ya sa suka ga ya dace su karrama shi.
Daga nan ya ce Gwamnan ya raba musu Alkur’anai masu yawa a tsangayoyinsu kuma duk Sallah ko ta azumi ko Babbar Sallah suna shaidawa shi ya sa suka nuna godiyarsu ta hanyar ba shi wannan lambar girma.
“Da yake mu mahaddatan Alkur’ani ne a jikin lambar yabon mun zana allo  muka yi masa ado tare da rubuta wata aya a jiki muka ba shi a matsayin lambar yabo shaidar cewa mu Alarammomi ne ke nan,”inji shi.
Har ila yau, ya nemi gwamnati ta bullo musu da wata hanya ta koyar da almajiransu wajen kebe su a waje daya don yin karatu, ta samar wa  malamansu matsuguni da zai sa almajiransu yi karatunsu cikin natsuwa.
A karshe ya ce kungiyar  tana bukatar a samar mata da wajen da za ta gina babbar sakatariyarta mai dauke da ofisoshi da dakin taro wanda idan taro na kungiyar ya taso za su  gudanar  a wajen ba tare da sai sun fita wani waje daban ba.