Kungiyar ALGON ta zargi Gwamnan Zamfara da rike kudadensu

Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi, ALGON, reshen Jihar Zamfara, ta zargi gwamnatin jihar da rike wa Kananan Hukumonin jihar kason kudadensu da suka samu daga Asusun Rabon Arzikin Kasa, duk kuwa da umurnin da shugaba Buhari ya bayar na a tura wa Kananan Hukumomin Kasar nan kason su kai kai tsaye zuwa asusun Kananan Hukumomin. Da […]

Kungiyar ALGON ta zargi Gwamnan Zamfara da rike kudadensu

Gwamna Muhammad Bello Matawalle na jihar Zamfara

Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi, ALGON, reshen Jihar Zamfara, ta zargi gwamnatin jihar da rike wa Kananan Hukumonin jihar kason kudadensu da suka samu daga Asusun Rabon Arzikin Kasa, duk kuwa da umurnin da shugaba Buhari ya bayar na a tura wa Kananan Hukumomin Kasar nan kason su kai kai tsaye zuwa asusun Kananan Hukumomin.

Da yake yi wa wani taron manema labarai jawabi a Gusau, babban birnin Jihar, Kakakin Kungiyar reshen jihar ta Zamfara, Alhaji Ahmed Abubakar, ya yi zargin cewa, gwamnatin jihar ta ki yin amfani da umurnin shugaban kasa, inda ta yi karan tsaye ta hanyar yin kememe wajen kin sakarwa Kananan Hukumomin jihar kasonsu.

 

Ya ce: “Mun kadu sosai, da jami’an gwamnatin jiha suka shaida mana bayan taron wata-wata na Asusun Hadaka, cewa bayan da aka biya albashi da cire haraji, an basu umurnin su bai wa kowane shugaban Karamar Hukuma Naira Miliyan 5, dan gudanar da Ayyukan Karamar Hukuma, cikin kwanaki 30 masu zuwa.”

“Mun shaida musu cewa, hakan ya ci karo da umurnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar, amma sun ki su saurare mu.” In ji shi.