kungiyar Amnesty ta koka kan tsare wakilin rediyon RFI
kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Amnesty International ta koka kan ci gaba da tsare wakilin sashen Hausa na gidan Rediyon Faransa (RFI) da Gwamnatin Kamaru ke yi har tsawon watanni uku ke nan. A duk tsawon wannan lokaci ba a yarda wani mutum ya kai wa dan jaridan mai suna, Ahmad Abba, ziyara ba, […]
kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Amnesty International ta koka kan ci gaba da tsare wakilin sashen Hausa na gidan Rediyon Faransa (RFI) da Gwamnatin Kamaru ke yi har tsawon watanni uku ke nan.
A duk tsawon wannan lokaci ba a yarda wani mutum ya kai wa dan jaridan mai suna, Ahmad Abba, ziyara ba, koda ko lauyansa ne.
A kan wannan kungiyar ta nemi gwamnati ta yi bayani game da halin da yake ciki da kuma inda yake tsare. Kamar yadda kungiyar ta bayyana, hukumomi sun tsare Ahmad tun ranar 28 ga watan Yulin bana a birnin Maroua a lokacin da yake gudanar da bincike da ya dangaci ta’addancin da kungiyar Boko Haram take haddasawa a lardin Arewa-mai-Nisa na kasar. Har a yanzu kuma ba a tuhume shi da aikata wani laifi ba. Wannan ya sa kungiyar ta ce ko da wani irin laifi ma ya aikata, bai kamata a tsareshi a sirrance ba. Ta ce hakan ya saba wa dokokin kasa-da-kasa.
A martanin da gwamnatin Kamaru ta yi, Kakakin Gwamnati Minista Issa Tchiroma Bakary ya ce “Tsare wakilin gidan rediyon da aka yi bai saba wa doka ba. Sa’annan kuma ba a taka hakkinsaba. An tsare shi ne karkashin dokar yaki da ta’addanci. Ba a tsare shi saboda shi dan jarida ne,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa: “saboda haka a yanzu babu ta yadda za a yarje kowa ya ziyarce shi domin hakan ka iya kawo cikas wurin binciken da ake gudanarwa. Sai bayan an kammala hakan ne za a mika shi ga kotu, inda za a yi ma sa shari’a,” inji shi.
Sai dai lauyan dan jaridan ya ce: “Mun rubuta wa Shugaban Kamaru da kuma Ministan Shari’ar kasar wasika, domin bayyana halin da Ahmed yake ciki, amma ba mu samu amsa ko guda ba daga gare su. Wannan ya saba wa dokar kasa da kuma dokokin aikinmu,” inji shi.