kungiyar Ansarul Faidhatul Tijjaniyya yi wa kasa addu’a
kungiyar Ansarul Faidhatul Tijjaniyya da ke garin Kafanchan ta gudanar da taron zikirin shekara da yi wa kasa addu’a da ta saba shiryawa kowace shekara a babban masallacin jumma’a da ke kofar fadar mai martaba sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad (CON). Malam Danladi Abubakar da Malam Aminu kassim ne suka gabatar da jawabi […]
kungiyar Ansarul Faidhatul Tijjaniyya da ke garin Kafanchan ta gudanar da taron zikirin shekara da yi wa kasa addu’a da ta saba shiryawa kowace shekara a babban masallacin jumma’a da ke kofar fadar mai martaba sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad (CON).
Malam Danladi Abubakar da Malam Aminu kassim ne suka gabatar da jawabi ga mahalarta taron kan falalar taruwa a dakin Allah don ambaton Allah da kuma tasirin da ambaton Allah da kuma addu’o’i kan haifar a gari da kuma kasa gaba daya inda su ka jawo hankalin jama’a kan komawa zuwa ga Allah don nemo mafita kan halin da kasa ke ciki.
A lokacin da yake zantawa da Aminiya bayan kammala zikiri da addu’o’in, shugaban kungiyar Ansarul Faidha, Alhaji Sulaiman Tijjani wanda mataimakinsa Alhaji Baballiya Musa Kalla ya wakilta don yin bayani ya shaidawa Aminiya cewa wannan kungiya an kafa ta ne don shiryawa da kuma gudanar da addu’o’i a watan farko na kowace shekarar musulunci wanda wannan shine karo na uku da su ka fara shirya irin wannan taro don yi wa kasa da kuma masarautar Jama’a addu’o’in zaman lafiya.
“Baya ga shirya addu’o’i da zikirin shekara mu kan tuntubi jagororin masallacin jumma’a kan wasu ayyuka da ake da bukatan yiwa masallacin domin aiwatarwa kamar sanya intalop da sauransu. Har ila yau daga cikin aikinmu akwai gyara masallatai da makarantun addini.”
Daga cikin mahalarta taron zikiri da addu’an na bana har da Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad da limamin Jama’a da na Kagarko da sauran jama’a da su ka zo daga garuruwan kudancin Kaduna da kuma Keffin dan Yamusa da ke Jihar Nasarawa.