Kungiyar APC ta zargi gwamnatin Kano da sayar da filin makaranta

Kungiyar Volunteers for Democracy, da ke jam’iyyar APC, ta zargi gwamnatin jihar Kano da jam’iyyar NNPP ke jagoranta da rushewa da kuma sayar da filin Makarantar Sakandare ta Maikwatashi da ke unguwar Sabon Gari a jihar.

Kungiyar APC ta zargi gwamnatin Kano da sayar da filin makaranta

APC

Kungiyar Volunteers for Democracy, da ke jam’iyyar APC, ta zargi gwamnatin jihar Kano da jam’iyyar NNPP ke jagoranta da rushewa da kuma sayar da filin Makarantar Sakandare ta Maikwatashi da ke unguwar Sabon Gari a jihar.

Sai dai gwamnatin jihar ta musanta wannan zargi, tana mai cewa tana kokarin canza wa makarantar wuri ne zuwa wurin da ya fi aminci zuwa unguwar Kaura Goje, ba wai sayar da ita don samun kuɗin filin ba.

Amma a yayin taron manema labarai a Kano ranar Lahadi, yayin taron shugabannin ƙungiyar na jiha, Sakataren ƙungiyar, Ibrahim Dan-Azumi Gwarzo, ya ce dalilan da aka bayar na canza wa makarantar matsuguni da zargin sayar da ita ba shi da ƙarfi.

Gwarzo ya ce, “Jami’an gwamnati sun fito suna kare canza wa makarantar wuri da aka yi, wasu ma na zargin cewa an sayar da makarantar gaba ɗaya a farashi mai tsada. Sun ce wurin ba shi da aminci ga makaranta, shin hakan na nufin duk makarantar da ke cikin irin wannan hali za a sayar da ita ke nan?

“Gwamnati ba ta musanta cewa ta sayar da wurin ba, sai dai tana cewa za ta yi amfani da shi yadda ya dace. To ina yaran za su ci gaba da karatu kafin a kammala sabon ginin makarantar da za a canza wa waje?

“Wannan fa na faruwa ne a lokacin da UNICEF ke kuka kan karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar. Gwamnati ce ma ta zargi Ganduje da irin wannan matsalar, amma ita ma tana yin abin da ya fi nata,” in ji shi.

Tun da farko, Shugaban ƙungiyar, Alhaji Usman Alhaji, ya nuna damuwa kan abin da ya kira rashin gaskiya da rikon amana a gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Alhaji, wanda ya rike mukamin Sakataren Gwamnatin Kano zamanin mulkin Ganduje, ya ce, “Akwai rahotannin kafafen yaɗa labarai kan yadda ake zargin an karkatar da biliyoyin kuɗaɗen jama’a ba bisa ka’ida ba. Binciken da EFCC da ICPC ke yi, da wasu shari’u da ke a gaban kotu, abin damuwa ne,” in ji Alhaji.

Ya kuma koka kan halin da makarantu, asibitoci, hanyoyi da samar da ruwa sha ke ciki a jihar duk da cewa kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke tura wa jihar sun karu.

Sai dai Alhaji ya yaba wa Gwamna Yusuf kan biyan haƙƙin sallama ga tsofaffin kansiloli, har da waɗanda suka yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin Ganduje ta APC, da kuma gyaran titunan da ake yi a cikin birnin Kano.

Kungiyar ta kuma sanar da ƙaruwar yawan mambobinta, wanda yanzu ta ce sun kai 110,000, yayin da suke burin adadin zai kai 500,000 kafin zaɓen 2027.