Kungiyar ASUU ta dawo aiki ko ta ci gaba da yajin aiki har a biya bukatunta?
A daidai lokacin da ake ci gaba da kai-komo a kan cimma matsaya tsakanin kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) da Gwamnatin Tarayya kan yajin aikin da ta kira, wadansu na cewa idan giwaye biyu na fada, ciyawa ce ke shan wahala. Don haka suke ganin ASUU ta hakura a dawo bakin aiki, yayin da wadansu ke […]
A daidai lokacin da ake ci gaba da kai-komo a kan cimma matsaya tsakanin kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) da Gwamnatin Tarayya kan yajin aikin da ta kira, wadansu na cewa idan giwaye biyu na fada, ciyawa ce ke shan wahala. Don haka suke ganin ASUU ta hakura a dawo bakin aiki, yayin da wadansu ke cewa kawai malaman su ci gaba da yajin aiki har sai gwamnati ta biya musu bukatunsu. Wannan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’yoyin mutane, kamar haka:
Su janye yajin aikin – Anas Saminu
Daga Abbas Dalibi, Legas
Malam Anas Saminu Ja’en: “A gaskiyar magana ya kamata a ce idan da gaske gwamnati ke yi na kawo ci gaban ilimi a kasar nan, to ya kamata a ce malamai sun daina yin wani abu wai shi yajin aiki a biya musu bukatunsu daidai da yadda za su yi rayuwa su da iyalansu. Duk da kasancewar gwamnati ta sha zama da Kungiyar ASUU kuma ana bakin kokari wajen ganin yajin aikin ya zo karshe abin ya ci tura, me zai hana su malam su duba wani abu guda daya wato taimakon ’ya’yan talakawa da suke yi wajen koyarwa. Yanzu haka sun tsayar musu da karatu yara na gida babu abu guda daya da suka kama, ina ganin idan suka yi haka sai su ci gaba da tattaunawa da gwamnati yin hakan zai iya sa wa Allah Ya shiga cikin lamarin bukatarsu ta biya. Ya kamata a duba bukatun daliban nan da suke zaune a gida yanzu, domin haka da gwamnatin da su malamam suna nuna rashin ko’in kula a karatun ’ya’yan talakawa ne saboda ’ya’yansu suna kasashen Turai suna karatu, ga ’ya’yan talakawa sun yi birus da su. Su sani Allah ne Ya ba su wadannan dama ba don su cutar da kowa ba ko kuma musguna wa kowa ba, Allah Yana kallon kowa da duk abin da wani ya aikata. Don haka a ra’ayina su janye yajin aikin su koma bakin aiki su ci gaba da tattaunawa da gwamnati ko Allah Ya sa ta ji kukansu.
A janye yajin aiki daga baya a tattauna – Muhammad Kabir Magaji
Daga Rabilu Abubakar, Gombe
Muhammad Kabir Magaji: “A nawa ra’ayin gara malaman jami’a su koma aiki don yajin aikin ba alheri ba ne lura da halin da kasar take ciki. Duk wani zama da gwamnati za ta yi da malaman gara yaran suna karatu saboda wadansu sun kusa kammala karatun, yajin aikin zai mayar musu da karatu baya. Malaman su rika hakuri da abin da suke samu saboda har yanzu kasar a karkace take ba ta gama zama ba.”
Malaman suna cutar da yaranmu ne ba gwamnati ba –Buhari Zakari
Daga Hussaini Isah, Jos
Alhaji Buhari Zakari Wazirin Kaffe: “Wannan yajin aiki da malaman jami’o’i suke yi abin dubawa ne, domin malaman nan ba wai suna cutar da Gwamnatin Tarayya ba ce, suna cutar da yaranmu ne da su baki daya. Wannan yajin aiki ba ya shafar manya kasar nan saboda ’ya’yansu ba sa zuwa makarantun gwamnati. Akasarin yaransu suna karatu a kasashen waje ne. Don haka wannan yajin aiki yana shafar ’ya’yan talakawa ne da malamai baki daya. Don haka ina ganin malaman nan su tausaya wa ’ya’yan talakawa su yi hakuri su koma wajen aikinsu. Ita kuma gwamnati ta duba bukatunsu, idan ba za ta iya biya baki daya ba, ta biya wasu daga ciki.”
Gaskiya su koma aji – Hadiza Ibrahim
Daga Abbas Dalibi, Legas
Hadiza Ibrahim: “A gaskiya dai ya kamata su koma bakin aiki su ci gaba da koyarwa domin rashin komawarsu aiki zai shafi karatun ’ya’yan talaka, wannan ba daidai ba ne, idan suka koma bakin aiki sai ka ga albarkacin ’ya’yan talaka Allah Ya taimake su gwamnatin ta saurares u ta biya musu bukatarsu.”
Janye yajin aikin sai su ci gaba da tattaunawa – Mamuda Mai Taki
Daga Rabilu Abubakar, Gombe
Mamuda Mai Taki Kwadom: “Yajin aikin bai da amfani gara su janye yara su koma makaranta, in ya so a tattauna a hankali har a shawo kan matsalar. Zaman daliban a gida yana haifar da koma baya da cikas a harkar karatunsu domin duk inda yara suka zauna a gida ya yi yawa suna manta abin da suka karanta. Sannan kuma ya kamata gwamnati ta duba wannan lamari.”
Yajin aikin malaman ba alheri ba ne – Habibu Abubakar
Daga Hussaini Isah, Jos
Alhaji Habibu Abubakar: “Maganar gaskiya ya kamata malaman su janye yajin aikin da suke yi su dawo su ci gaba da aikin karantar da dalibansu. Domin yajin aikin da suke yi ba alheri ba ne. Babu wanda yake cutuwa a wannan yajin aiki, sai ’ya’yan talakawa domin shugabannin ’ya’yansu ba sa karatu a Najeriya. Idan ma suna karatu a Najeriya suna yi ne a makarantu kudi. ’Ya’yan talakawa ne kawai suke karatu a na gwamnati. Saboda haka ya kamata malaman jami’o’in su duba wannan al’amari su janye wannan yajin aiki. Domin wannan aiki na su ai sadakatul jariya ce, ba wai suna yi ne don kudi ba, abin da suke yi ya fi karfin kudi. Don haka ya kamata su duba halin da talakan Najeriya yake ciki su tausaya su dawo kan aiki. Su kuma gwamnati ya kamata su ji tausayin malaman nan, su duba bukatunsu. Tun daga kan Shugaban Kasa har zuwa gwamnonin Najeriya da ministoci malamai ne suka karantar da su, amma yanzu cikinsu babu malamin makaranta.”