Kungiyar ASUU ta dawo aiki ko ta ci gaba da yajin aiki har a biya bukatunta?
Sarkin Fulanin Jihar Kwara, Alhaji Usman Adamu ya ce kalubale mafi girma da al’ummar Fulani makiyaya ke fuskanta a kasar nan shi ne rashin ilimi. Sarkin Fulanin ya bayyana haka ne jim kadan bayan da Mai martaba Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari ya naɗa shi Sarkin Fulanin Jihar Kwara a ranar Juma’ar da ta […]
Sarkin Fulanin Jihar Kwara, Alhaji Usman Adamu ya ce kalubale mafi girma da al’ummar Fulani makiyaya ke fuskanta a kasar nan shi ne rashin ilimi.
Sarkin Fulanin ya bayyana haka ne jim kadan bayan da Mai martaba Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari ya naɗa shi Sarkin Fulanin Jihar Kwara a ranar Juma’ar da ta gabata, bayan rasuwar Sarkin Fulanin Jihar, Hardo Buruku kimanin shekara biyu da suka shude.
Ya ce duk matsalolin da al’ummar Fulani kan samu kansu a ciki a yanzu, suna samuwa ne sakamakon rashin ilimin makiyaya, don haka suka zamo koma baya aka mayar da su saniyar ware.
“Mu Fulani mutane ne masu asali, masu yalwar arziki kuma a baya can mu mutane ne masu ilimi da sanin muhinmmancinsa domin kakkaninmu ne suka yada ilimin addinin Musulumci a kasar nan, sai dai a yanzu al’ummarmu na cikin duhun jahilci na ilimin addini da na zamani, wannan shi ne babban kalubalenmu. Don haka wannan lamari zan fuskanta domin ganin mun dora al’ummarmu a kan turbar ci gaba,” inji shi.
Sabon Sarkin Fulanin ya sha alwashin daukar matakin farfado da ilimin ’ya’yan Fulani makiyaya, ya ce zai hada karfi da karfe da sauran shugabannin Fulanin yankin wajen farfado da harkar ilimin ’ya’yan Fulani makiyaya.
“Domin idan ka bai wa al’umma ilimi ka yi mata komai.t Tun lokacin da nake jagorantar kungiyar Fulani makiyaya ta Miyyati Allah a nan Jihar Kwara mun yi ƙoƙarin kafa makarantun Fulani makiyaya a wasu rugagenmu sannan mun ba da gagarumar gudunmawa wajen ganin an samu zaman lafiya tare da dakile miyagun ayyukan masu yin garkuwa da mutane suna karbar kudin fansa. A wannan aiki da na jagoranta an yi barazanar hallaka ni, amma komai nufi ne na Allah tunda bai kaddara kwanana ya kare ba a wancan lokacin, don haka wannan dama da Allah Ya ba ni zan yi amfani da ita wajen inganta rayuwar al’ummarmu don haka nake neman goyon bayansu baki daya da su zo mu yi aiki tare domin ci gaban al’ummarmu,” inji shi.
Mai martaba Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari ya umarci sabon Sarkin Fulanin ya zamo mai biyayya ga masarautar Ilori kuma ya ci gaba da jajircewa domin ci gaban al’ummar yankin kamar yadda ya saba, ya ce al’ummar Jihar Kwara guda ce ba sa nuna bambancin ƙabila ko na addini, ya ce zuri’ar Shehu Usmanu Dan Fodiyo ce ke mulkin jihar tun daga kan Shehu Alimi.