kungiyar ASUU ta janye yajin aiki ta likitoci ta farakungiyar ASUU ta janye yajin aiki ta likitoci ta fara
kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU), ta janye yajin aikin da ta kwashe watan biyar tana yi domin neman gwamnati ta inganta ilimin jami’a.Shugaban kungiyar na kasa Dokta Nasiru Fagge ne ya bayyana janye yajin aikin a taron manema labarai da ya gudanar a Jami’ar Fasaha da kere-kere ta Tarayya (FUT) da ke Minna fadar […]
kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU), ta janye yajin aikin da ta kwashe watan biyar tana yi domin neman gwamnati ta inganta ilimin jami’a.
Shugaban kungiyar na kasa Dokta Nasiru Fagge ne ya bayyana janye yajin aikin a taron manema labarai da ya gudanar a Jami’ar Fasaha da kere-kere ta Tarayya (FUT) da ke Minna fadar Jihar Neja a ranar Talatar da ta gabata.
Dokta Nasir Fagge ya ce ASUU ta dakatar da yajin aikin ne bayan cimma matsaya da Gwamnatin Tarayya da kuma amincewar mambobinta.
An yi ta kai ruwa rana tsakanin gwamnati da kungiyar ASUU kan yajin aikin inda Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar korar daukacin malaman jami’o’in kasar idan suka gaza komawa bakin aiki kafin wa’adin da ta deba musu, sai dai barazanar ba ta yi tasiri ba.
Ranar 1 ga Yulin da ya gabata ne ASUU ta shiga yajin aikin domin da matsa wa gwamnati ta cika alkawurran da ta dauka wa kungiyar a yarjejeniyar da suka kulla a shekarar 2009.
A wani labarin kuma kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) ta fara yajin aikin jan kunne na yini biyar a shekaranjiya Laraba, inda ta bukaci a inganta yanayin aiki a bangaren kiwon lafiya.
Shugaban kungiyar Dokta Osahon Enabulele ne ya bayyana haka, inda ya shaida wa Aminiya ta waya cewa duk da cewa sun sanya hannu kan yarjejeniya da masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya bayan shafe awa 14 ana ganawa kungiyar NMA ba ta tattauna ta yanke shawara kan yarjejeniyar ba.
Dokta Enabulele ya ce sun fara ganawa da misalin karfe 3:30 na yammacin ranar Litinin suka kare karfe 5 na safiyar Talata a ofishin Ministan kwadago, to amma ba za a janye yajin ba, saboda Majalisar Gudanarwar kungiyar ta kammala taronta a Minna a karshen mako tare da ba da umarnin a gudanar da yajin aikin jan kunnen.
Ya ce za su tattauna a kan yarjejeniyar a jiya Alhamis domin daukar mataki a kai, sai dai har zuwa hada wannan rahoto ba mu samu hukuncin da suka zartar ba.