Kungiyar AYCF ta yi tir da kama ’yan Arewa a Legas

Kungiyar Tuntuba ta Matasan Arewa (AYCF) ta yi tir da kamen ba gaira ba dalili da ta ce ana yi wa ’yan Arewa musamman masu sana’ar acaba a birnin Legas. A  taron ’yan jarida da Kungiyar AYCF ta yi a ranar Litinin da ta gabata a Unguwar Oshodi, Shugaban Kungiyar AYCF ta Kasa, Alhaji Yarima […]

Kungiyar AYCF ta yi tir da kama ’yan Arewa a Legas

Kungiyar Tuntuba ta Matasan Arewa (AYCF) ta yi tir da kamen ba gaira ba dalili da ta ce ana yi wa ’yan Arewa musamman masu sana’ar acaba a birnin Legas.

A  taron ’yan jarida da Kungiyar AYCF ta yi a ranar Litinin da ta gabata a Unguwar Oshodi, Shugaban Kungiyar AYCF ta Kasa, Alhaji Yarima Shatima ya yi kira ga Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta dubi lamarin inda ya nemi Gwamnatin Jihar Legas ta yi bayanin dalilin da ya sa jami’an tsaron na hadaka na tak-fos ke bin ’yan Arewa har cikin gidaje da tsakar dare suna kwashe musu baburansu, kuma suna kama su. “Muna kira ga Gwamnatin Legas ta sako jama’armu da ta kama su ba tare da laifin komai ba. Suna kwance a gidajensu cikin dare, jami’an Tak-fos na Legas suka far musu suka kwashe musu baburansu, yanzu haka suna tsare da sama da mutum 100 sannan sun kama babura 680 a cikin gidaje cikin dare. Gwamnatin Legas ba ta haramta sana’ar acaba ba, ta hana amfani da babura ne a wasu manyan hanyoyin jihar. Don haka ban ga dalilin da zai sa a biyo mutum har cikin gidansa a kwace masa abin sana’arsa, sannan a kama shi ba,” inji shi.

Alhaji Yarima Shatima, ya yi kira da Gwamnatin Legas ta kiyayi cin zarafin ’yan Arewa mazauna jihar domin yin haka na iya jawo barazana ga tsaron kasa.

Hukumar Tak-fos ta Legas ce a karkashin jagorancin CSP Yinka Ogbeyemi ta kai farmaki kan masu baburan, inda ya fitar da bayanin cewa, an raunata jami’in hukumar guda a lokacin da suka kai farmakin.