kungiyar AYF ta koka kan tabarbarewar tsaro a Arewa
kungiyar da ke fafutukar kwato ’yancin ’yan Arewa (Arewa Youth Foundation –AYF) da ke Jihar Legas ta ce rashin tsaro a yankin Arewa ne babbar matsalar da ke ci mata tuwo a kwarya.Babban sakataren tsare-tsaren kungiyar, Alhaji Musa Shabiri shi ne ya yi furucin haka a yayin da yake tattaunawa da Aminiya a ofishin kungiyar […]
kungiyar da ke fafutukar kwato ’yancin ’yan Arewa (Arewa Youth Foundation –AYF) da ke Jihar Legas ta ce rashin tsaro a yankin Arewa ne babbar matsalar da ke ci mata tuwo a kwarya.
Babban sakataren tsare-tsaren kungiyar, Alhaji Musa Shabiri shi ne ya yi furucin haka a yayin da yake tattaunawa da Aminiya a ofishin kungiyar da ke yankin Apapa kwanan baya.
Alhaji Musa ya ce, “A gaskiya, mu babban abin da yake damun mu shi ne maganar Najeriya baki daya, musamman ma abin da yake faruwa a yankinmu na Arewa, saboda a nan Kudu muna zaune lafiya, babu abin da yake tayar mana da hankali. Saboda haka muna kira ga shugabaninmu na Arewa su fito su yi maganin wannan matsala, kodayake an ce gwamnati ta dauki mataki, ya kamata a kara tsaurara matakan tsaro, wanda rashinsa ne ya sa wasu suka shiga barikin soja suka kai hari. Ka ga wannan ya nuna cewa babu tsaro a Najeriya domin kamata ya yi a ce akwai na’urar da za ta gano masu kai hari tun daga nesa ba sai sun shigo cikin bariki ba”.
Ya ci gaba da cewa, “Muna kira ga gwamnoninmu na Arewa su tashi su yi wani abu a kan wadannan abubuwa don ya kamata a ce tuni sun dauki mataki. Idan ka duba za ka ga cewa matasa aka fi kashewa a wannan lamari. Shi ya sa muke ganin kamar ma akwai wata kulalliya da ake yi wa Arewa don a gama da samarinta baki daya”.
Da yake karin bayani, sakataren yada labarai na kungiyar, Malam Muhammadu Nura Wagani ya ce burin da kungiyar take so ta cimma sun hada da bunkasa matasa da kare hakkinsu a Legas, kuma tana da ajandodin da ta tsara don ci gaban matasan Arewa da ke zaune a Jihar Legas.
Shi ma a nasa jawabin, babban mai binciken kudi na kungiyar, Malam Abubakar Muhammed ya ce yin gaskiya da hakuri da rikon amana da shugabannin kungiyar suka rike shi ya sa kungiyar take samun nasara a ayyukanta.