kungiyar Babbangida ta yi taronta karo na 3 a Kano
kungiyar sada zumunta na WhatsApp Group mai suna, Babbangida ta yi taronsa na uku a Gidan Magi da ke unguwar Hotoro ta Jihar Kano, inda mambobin kungiyar sama da 100 suka samu halarta.Bayan kammala taron ne Aminiya ta samu zantawa da wanda ya assasa wannan kungiyar, El-Mansur Yusha’u Muhammad, wanda ake wa lakabi da Babban […]
kungiyar sada zumunta na WhatsApp Group mai suna, Babbangida ta yi taronsa na uku a Gidan Magi da ke unguwar Hotoro ta Jihar Kano, inda mambobin kungiyar sama da 100 suka samu halarta.
Bayan kammala taron ne Aminiya ta samu zantawa da wanda ya assasa wannan kungiyar, El-Mansur Yusha’u Muhammad, wanda ake wa lakabi da Babban Yaya, don jin dalilansa na kafa wannan kungiya ta Babbangida.
El-Mansur ya ce abin da ya sa shi ya kafa wannan kungiya ko zaure shi ne tun yana karami shi son mu’amulla ne da mutane ga kuma son barkwanci da wasa da dariya shi ya sa ya bude shafin sada zumunta na Facebook har aka samu ci gaba a manhajar WhatsApp.
“Na fara mu’amalla ta da wasu daga cikin wadannan jama’ar ne tun ta shafina na Facebook kafin yanzu mu sake haduwa a wannan kungiya ta WhatsApp da na sawa suna Babbangida kuma magoya bayan nawa a Facebook din ganin irin kyakkyawar manufa da nake da ita a shafin nawa ya sa suka biyo ni WhatsApp muka ci gaba da sada wannan zumunci,” inji shi.
Daga nan ya ce: “Babban burina a wannan kungiya shi ne nan ba da jimawa ba a fara samun auratayya a tsakanin mambobin kungiyar maza da mata wanda in Allah Ya yarda. Kuma za a samu hakan domin akwai wadanda suke kaunar juna da auren.”
Ya ce, “lakabin Babban Yaya matan kungiyar ne suka sa mini duk da cewa ma da yawa a kungiyar sun girmeshi tun yana kin sunan har wasu mutane suka kirashi suka ce mini ya karbi sunan ba don ya fi so ba sai don darajar wannan kungiya da ya samu, hakan ne kawai ya sa na amince yake amsa sunan.”
Har ila yau, ya bukaci daukacin mambobin kungiyar da su daraja juna su dinga yin hakuri saboda a baya ba’a san juna ba, amma yanzu an zama ’yan uwan juna a cewarsa.
Ya ce an kafa kungiyar ne da mambobi 16 daga baya suka kai 50 yanzu haka kuma tana da mambobi guda 100 ne.
Taron tun farko a Jihar Gombe aka shirya yinsa, amma halin rashin tsaro ya sa aka dawo da shi Jihar Kano duk cewa taron kungiyar na a farko ma a Kano din aka yi a Gidan Magi, sai taro na biyu aka yi a garin Saminaka ta Jihar Kaduna. Kodayake, taro na gaba wanda za su yi lokacin Babbar Sallah shi ne wanda aka shirya yi a Jihar Gomben.