kungiyar BCO ta nemi Buhari ya sallami masu yi masa zagon kasa

Wata kungiya da ke ikirarin kare martabar Shugaban kasa  Muhammadu Buhari da a takaice ake kira BCO ta bukace shi ya kori wadanda suke yi wa gwamnatinsa zagon kasa kan batun tallafa wa ’yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu a Jihar Barno.Shugaban matasan kungiyar na kasa, Abdulhamid dankyarko ne ya […]

kungiyar BCO ta nemi Buhari ya sallami masu yi masa zagon kasa
kungiyar BCO ta nemi Buhari ya sallami masu yi masa zagon kasa

Wata kungiya da ke ikirarin kare martabar Shugaban kasa  Muhammadu Buhari da a takaice ake kira BCO ta bukace shi ya kori wadanda suke yi wa gwamnatinsa zagon kasa kan batun tallafa wa ’yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu a Jihar Barno.
Shugaban matasan kungiyar na kasa, Abdulhamid dankyarko ne ya bayyana haka, lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Abuja a karshen makon jiya.
“Duk kokarin da Shugaban kasa yake yi na ganin ya kawo karshen matsalar da ’yan gudun hijirar suka shiga sai ga shi an samu wadansu jami’ai a gwamnatinsa suna yi masa zagon kasa ta hanyar kin sakin kudaden da ya bayar da umarnin a bai wa ’yan gudun hijirar. Saboda haka muna kira gare shi ya kori irin wadannan jami’ai daga mukamansu,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa “Muna kira ga Shugaban kasa ya sallami wadansu mukarrabansa da ake zargi da zaunawa a kan fayil din da ya sanya wa hannu ya bayar da umarnin a fitar da Naira biliyan hudu a tallafa wa ’yan gudun hijirar.”
dankyarko ya yi zargin cewa zagon kasan da wadannan jami’an gwamnati ke yi ne ya jawo shiga halin tsaka-mai-wuya da ’yan gudun hijirar suka shiga a sansanoni da dama a Jihar Barno.
Ya ce ya zama wajibi Shugaban kasa ya dauki matakan gaggawa kan irin jami’an da suke yi masa zagon kasa tun kafin lokaci ya kure.
Ya ce muddin Shugaban kasa bai dauki matakin gaggawa na sallamar su ba, to babu shakka lamarin zai iya shafar dawowarsa mulki a shekarar 2019.
Ya bayyana cewa yana da shaidu da hujjoji da zai gabatar wa duk wanda yake musun zargin da ya yi.
Ya ce ’yan gudun hijira na cikin tsaka mai wuya saboda yunwa da wahalar rayuwa da suka shiga.