kungiyar Bunkasa Adabi za ta karrama Dokta Bukar Usman a taronta

kungiyar Bunkasa Adabin Gargajiya Ta Najeriya (Nigerian Folklore Society of Nigeria) ta sadaukar da babban taronta na bana domin karrama sanannen marubucin tatsuniyoyin Hausa, Dokta Bukar Usman (OON).Babban taron, wanda za a gudanar da shi a Jami’ar Bayero Kano daga ranar 2 zuwa 4 ga watan gobe, zai tattara masana da dalibai da sauran masu […]

kungiyar Bunkasa Adabi za ta karrama Dokta Bukar Usman a taronta

kungiyar Bunkasa Adabin Gargajiya Ta Najeriya (Nigerian Folklore Society of Nigeria) ta sadaukar da babban taronta na bana domin karrama sanannen marubucin tatsuniyoyin Hausa, Dokta Bukar Usman (OON).
Babban taron, wanda za a gudanar da shi a Jami’ar Bayero Kano daga ranar 2 zuwa 4 ga watan gobe, zai tattara masana da dalibai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar Adabin Gargajiya, inda za su gabatar da takardu da sauran nazarce-nazarce da suka shafi adabi.
Kamar yadda tsarin taron zai gudana, Farfesa G.G. Dara na Jami’ar Jihar Delta ne zai gabatar da babban jawabi. A jawabin nasa, zai gabatar da takarda mai taken: ‘Tasirin Tatsuniyoyi da almara: Jiya Da Yau Da Gobe.’
Sauran masanan da za su gabatar da takardun nazari sun hada da Farfesa Zikky Kofoworola na Jami’ar Ilorin da Farfesa Bade Ajuwon na Jami’ar Obafemi Awolowo, Ibadan da sauransu. Takardun nasu za su tattauna ne game da maudu’o’i iri daban-daban da suka shafi Adabin Gargajiya, batun rubuce-rubuce da sassake-sassake da zayyana da sauransu.
A ta bakin Farfesa Sani Abba Aliyu, Babban-Sakataren kungiyar Bunkasa Adabin Gargajiya Ta Najeriya, an shirya taron ne da nufin farfado da aikace-aikacen kungiyar. Haka kuma ya bayyana cewa taron zai maida hankali ne kacokan wajen tatsuniyoyi da almara, wadanda a cewarsa, su ne jigo ko ginshikin Adabin Gargajiya, wadanda kuma suka fi shahara da amsuwa ga al’umma.
“Duk da muhimmanci da shaharar tatsuniya da almara a cikin al’umma, abin takaici shi ne ba a ba su muhimmancin da ya cancance su a fagen nazari.” Inji Babban- Sakataren.
Shi kuwa Dokta Bukar, wanda kungiyar ta sadaukar da taron da nufin karrama shi, ya kasance Babban-Sakatare a Gwamnatin Tarayya mai ritaya, wanda ya sadaukar da lokacinsa wajen rubuce-rubuce da kuma tallafa wa al’umma ta fannin ilimi da sauransu. Ya rubuta littattafai sama da guda ashirin, cikinsu har da babban kundin tatsuniyoyin Hausa da ya kunshi littattafai goma sha hudu da ya sanya wa suna ‘Taskar Tatsuniyoyi.’ A kwanakin baya ma wasu kungiyoyin marubuta biyu daga Najeriya da Nijar sun karrama shi a matsayin marubucin da ke tallafa wa harshen Hausa.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan

Tags