kungiyar CAPP ta koka kan karancin malamai mata
kungiyar bunkasa al’umma da ake kira da harshen Inglishi, Community Action For Popular Participation, (CAPP), ta ce babban kalubalen da makarantun gwamnati suke fuskanta a kauyuka shi ne na karancin malamai mata. Shugabar kungiyar CAPP, Kyauta Giwa ita ce ta yi furucin yayin da take tattaunawa da Aminiya a ofishinta da ke Abuja a karshen […]
kungiyar bunkasa al’umma da ake kira da harshen Inglishi, Community Action For Popular Participation, (CAPP), ta ce babban kalubalen da makarantun gwamnati suke fuskanta a kauyuka shi ne na karancin malamai mata.
Shugabar kungiyar CAPP, Kyauta Giwa ita ce ta yi furucin yayin da take tattaunawa da Aminiya a ofishinta da ke Abuja a karshen makon da ya gabata.
Ta ce, makarantun karkara na fama da karancin malamai musamman ma malamai mata.
Ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta kaiwa makarantun daukin gaggawa don inganta ilimi a karkara.
“Idan ka je makarantun firamare da na sakandare da ke yankunan karkara za ka tarar suna da karancin malamai musamman malamai mata. Kuma rashin malamai mata shi ke janyo wa yaran da ke makarantun ba su sha’awar koyarwa idan sun kammala karatu saboda ba su ganin mata da yawa suna koyarwa a makarantunsu. Da ka tambaye su me suke so su zama sai su ce aikin asibiti saboda suna ganin mata ma’aikatan asibiti sanye da Inifom suna tafiya aiki,” inji ta.
Ta bayyana cewa kungiyarsu ta gano cewa rashin wurin zama ga malaman da kuma nisan da makarantun suka yi da kauyukan shi ya sa malamai da yawa ba su son su koyar a wuraren.
“Za ka tarar makarantun sun yi nisa da gari saboda haka idan aka tura malami za ka tarar sai ya sha wahala kafin ya samu wurin da zai rika kwana sannan kuma da nisan da makarantun suka yi ga garuruwan. Saboda haka shi ya sa idan aka tura malamai kauyuka sai ka ga sun bi duk hanyar da za su bi an mayar da su makarantun birane,” inji ta.
Ta ce, wannan ba karamar matsala ba ce kuma ya kamata gwamnati da dauki matakin da ya dace na maganin matsalar.
Daga nan sai ta ci gaba da cewa mafiyawan makarantun suna fuskantar matsalar rashin kayan karatu da bandaki da kuma ruwan sha.
Si dai ta cee kungiyar ta yi amfani da kwamitocin iyayen yara da kauyuka wajen samar da ruwan sha da gina bandakuna saboda amfanin dalibai.
Kodayake, ta koka kan yadda wasu daga cikin mutanen karkara ba su fahimci ayyukan kungiyar ba. Ta ce sau da dama idan suka ziyarci wata makaranta a karkara sai ka ga mutanen garin suna daukan kungiyar a matsayin “wata hukuma ta gwamnati.”