kungiyar ci gaban matasa da ke Malumfashi ta yi wa matasa nasiha
Shugaban kungiyar ci gaban matasa da ke Malumfashi (Malumfashi Youth Debelopment Association), Malam Auwal Ahmed ya ja hankalin matasan kasar nan da kada su sake yarda a yi amfani da su wajen tayar da rikice-rikice, musamman a lokutan zabe.Malam Auwal ya yi wannan nasiha ce bayan kungiyar ta kammala taronta kan wayar da kan matasa […]
Shugaban kungiyar ci gaban matasa da ke Malumfashi (Malumfashi Youth Debelopment Association), Malam Auwal Ahmed ya ja hankalin matasan kasar nan da kada su sake yarda a yi amfani da su wajen tayar da rikice-rikice, musamman a lokutan zabe.
Malam Auwal ya yi wannan nasiha ce bayan kungiyar ta kammala taronta kan wayar da kan matasa kwanan baya, inda ya nuna matasa su ne ake yawan gani a sahun gaba lokutan tashe-tashen hankula, wanda ko kadan hakan ba zai kawo alheri ga kasa ba .
“Kowa ya san matasa su ne kashin bayan ci gaban kowace kasa ta duniya, idan aka dubi matsayinsu ta fannoni daban-daban, amma sai a wayi gari kuma su ke kan gaba, idan wata tarzoma ta tashi. Idan matasa za su jajirce su kauce wa shiga rigingimu walau na siyasa ko na kabilanci ko dai makamantansu, ko shakka babu za a sami ingantaccen zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa”. Inji shi.
Sai dai ya yi kira ga gwamnatocin kasar nan da shugabanni su kara bullo da hanyoyin inganta rayuwar matasa ta yadda za su sami natsuwa da kasancewa kan tafarkin dogaro da kai. A karshe ya jaddada aniyar kungiyarsu ta ci gaba da aikin wayar da kan matasa ta yadda za a sami kyakkyawan gyara a kasar nan.