kungiyar cigaban garin Lawanti za ta gina Firamare
Garin Marori da ke yankin Lawanti a karamar hukumar Akko a Jihar Gombe gari ne mai dadadden tarihi da aka kafa shi sama da shekara 30 wanda ’ya’yan garin suna karatu har jami’a, amma garin bai taba mallakar koda ajin karatu ba. Amma yanzu za a gina musu makarantar firamare mai azuzuwan uku. Wannan yunkuri […]
Garin Marori da ke yankin Lawanti a karamar hukumar Akko a Jihar Gombe gari ne mai dadadden tarihi da aka kafa shi sama da shekara 30 wanda ’ya’yan garin suna karatu har jami’a, amma garin bai taba mallakar koda ajin karatu ba. Amma yanzu za a gina musu makarantar firamare mai azuzuwan uku.
Wannan yunkuri ya biyo bayan kokarin kungiyar cigaban garin Lawanti ne karkashin jagorancin Idris Maigari Lawanti, da sauran shugabanin kungiyar da suka hada kai da hukumar nan ta ci gaban al’umma CSDP Community and Social Debelopment Project.
Yanzu haka an dasa harsashin tubalin gina wannan makaranta wacce za ta lashe kudi naira miliyan biyar da dubu dari shida wanda kungiyar cigaban al’ummar garin na Lawanti suka samar da kashi goma cikin dari na kudin su kuma hukumar suka ba su kashi casa’in.
Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da aikin gina makarantar, Shugaban karamar hukumar Akko Alhaji Jani Adamu Bello, kira ya yi ga shugabannin wannan kungiya da su rike amana na wannan aiki da aka sa agaba kar don sun ga kudi su kashe su ba bisa ka’ida ba.
Alhaji Jani Bello, ya kuma yaba wa wannan hukuma ta CSDP na yadda su ka ga cancantar wannan gari na Marori wajen amincewa da su gina wannan makaranta wacce aka share sama da shekara 30 ana nema. Sannan sai ya ce shi ma da kansa ba zai zauna ya zuba ido ana yin abin da aka ga dama ba, zai sanya ido wajen kula da aikin don amfanar al’ummar garin na Marori.
Shi ma babban manajan hukumar Alhaji Abubakar Ardo Kumo, cewa ya yi irin ayyukan da wannan hukuma take gudanarwa a lungo da sako na fadin jihar ba za su kirgu ba, hakan kuma ya biyo bayan kason kudin da gwamnatin Jihar Gombe ta biya ne don samarwa al’umma ayyukan cigaba ta wannan hukumar.
Abubakar Ardo Kumo, ya godewa dan majalisar yankin Alhaji Gidado Lawanti na yadda ya hana su saka wajen ganin sai an samar da wannan makarantar a yankin domin a cewarsa duk wannan shekarun yara a gindin bishiya suke karatu kana daga bisani aka koma kofar gidan Jauron garin.
Shi kuwa manajan gudanarwa na CSDP Labilwa Isma’ila, kiran al’ummar garin na Marori ya yi da cewa a lokacin gudanar da wannan aiki su samu kwararren Injiniya wanda zai tsaya don ganin anyi aiki mai kyau wanda zai jima ana morarsa.
Idris Maigari Lawanti wanda shi ne shugaban kungiyar ci gaban al’ummar Lawanti, ya yi godiya bisa yadda ya samu hadin kan al’ummar wannan garin na Lawanti da Marori don ganin an samar da wannan makaranta don saukakewa al’ummar matsalar rashin makaranta.
Wannan aiki dai za a kammala shi ne a cikin wata biyu kuma za a gina bandaki irin na zamani.