kungiyar cigaban Hausawa
kungiyar cigaban al’ummar Hausawa a Jihar Oyo ta tara fiye da Naira dubu dari uku a wajen bikin kaddamar da asusun karasa aikin gina sabuwar sakatariyarta da ke Bodija, a birnin Ibadan. Bikin, wanda aka yi a ranar Lahadi, shi ne irinsa na farko tun bayan kafuwar kungiyar shekaru uku da wucewa. ’Ya’yan kungiyar daga […]

kungiyar cigaban al’ummar Hausawa a Jihar Oyo ta tara fiye da Naira dubu dari uku a wajen bikin kaddamar da asusun karasa aikin gina sabuwar sakatariyarta da ke Bodija, a birnin Ibadan. Bikin, wanda aka yi a ranar Lahadi, shi ne irinsa na farko tun bayan kafuwar kungiyar shekaru uku da wucewa. ’Ya’yan kungiyar daga sassa daban-daban na jihar sun halarci wajen bikin.
Cikin jawabin bude taro da Magajin garin Bodija, Alhaji Musa Abubakar Mai Buhu ya karanta, ya yi na’am da irin hobbasan da shugabannin kungiyar suka yi tun farko na samar wa kungiyar takardun rajista da tsare-tsarenta daga Abuja da sayen filin gina sakatariyar da aikin ginin da aka ci karfinsa, a cikin takaitaccen lokaci. “Ya kamata mu nuna musu farin cikinmu wajen ba su hadin kai da goyon baya, mu bayar da gudunmawar kudi da kayan aiki domin karasa wannan aiki, wanda za mu ci moriyarsa baki daya.” Inji shi.
Alhaji Musa ya ce, “Ya kamata mu lura da amfanin wannan kungiya, wadda ita ce ta farko da ta kafu bisa akidojin lalubo hanyoyin tallafa wa ’ya’yanta ta fannoni cigaban harkokin kasuwancinsu da sana’o’insu tare da kusantar mahukunta da ta samar wa kanta sakatariya. Saboda haka ina tabbatar da a shirye nake kan ba ta gudunmawa domin cigabanta.”
Shi kuwa Sarkin Hausawan Bodija, Alhaji Isyaka Bazamfare, ya yi alkawarin isar da sakon kungiyar ne ga dukkan kungiyoyin ’yan kasuwa da ke cikin babbar kasuwar Bodija, ta yadda Hausawa za su shige ta domin a tafi tare da su.
Shugaban masu fataucin wake daga Arewa zuwa Kudu na kasuwar Bodija, Alhaji Bala Kano jan hankalin ’ya’yan kungiyar ya yi su isar da sakon kungiyar ga sauran al’ummar Hausawa kan irin abubuwan alheri da ta tanadar domin amfanin Hausawa da ke zaune a jihar ta Oyo.
Da yake zagayawa da jama’a cikin sabuwar sakatariyar, sakataren kungiyar, Ustaz Tahir Zubairu ya ce bayan fiye da Naira dubu dari 3 da aka yi nasarar tarawa, akwai wasu mutane da suka yi alkawarin bayar da bandir-bandir na kwanon rufi da katako da makamantansu.
Ana sa ran kammala aikin ne kafin karshen shekara.