kungiyar Cigaban Zamfarawa ta koka kan matsalar matasa
kungiyar ci gaban Zamfarawa ta Jihar Zamfara ta koka da yadda a yanzu ake fuskantar lokacin zabe, la’akari da yadda wasu ’yan siyasa ke amfani da ’ya’yan jam’a, musamman talakawa suna ba su kudi don su sari matasa ’yan uwansu da makamai har abin ya kai ga kisa.Sakataren kungiyar, Malam Muhammad Kabir ya bayyana haka […]
kungiyar ci gaban Zamfarawa ta Jihar Zamfara ta koka da yadda a yanzu ake fuskantar lokacin zabe, la’akari da yadda wasu ’yan siyasa ke amfani da ’ya’yan jam’a, musamman talakawa suna ba su kudi don su sari matasa ’yan uwansu da makamai har abin ya kai ga kisa.
Sakataren kungiyar, Malam Muhammad Kabir ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gusau, dangane da babban abin da yake damunsu, wanda ya shafi yadda ake amfani da matasa wajen aikata mugayen laifuffuka kan kudi kalilan, wanda ba zai magance masu komai ba. “Su wadanda suke sanya su, ba za ka sami yaransu a ciki ba, shi ya sa kungiyarmu ta tashi tsaye don wayar da kan matasa don nuna musu illar abin da ake dora su a kai. Kuma kungiya na neman shirya hanyar da za a zauna da ’yan takara don nuna musu illar abin da suke yi. Matsalar matasan ita ce sukan manta cewa ko da akwai bambancin siyasa ko jam’iyya, ai garinsu guda ko karamar hukumarsu guda ko kuma jiharsu guda, balle kuma kasarsu daya”. Inji shi.
Sakatare Muhammad Kabir ya ce banda aikin wayar da kai kuma yana daga cikin aikin kungiya, ta rika ziyarar gidajen yari don fitar da wadanda suke tsare saboda bashi, musamman wadanda bashin ba bisa ganganci suka ci shi ba, ko kuma bai taka kara ya karya ba, wasu ma sai ka ga sun jima a gidajen kason.
Ya ce daga lokacin da suka kafa kungiyar sun sami nasarar fitar da mutane da dama.