Kungiyar daliban dambatta ta zabi sabbin shugabanni tare da karrama ‘ya’yanta
kungiyar daliban dambatta ta kasa ta zabi sabbin shugabannin kungiyar wadanda za su ja ragamar ta a shekarar 2018 zuwa 2019 tare da karrama wasu fitattaun mutane da ke ba harkar ilimi gudummowa a yankin. Da yake jawabi a wajen taron bikin, Hakimin dambatta kuma Sarkin Ban Kano Alhaji Muktar Adnan wanda ya sami wakilcin […]
kungiyar daliban dambatta ta kasa ta zabi sabbin shugabannin kungiyar wadanda za su ja ragamar ta a shekarar 2018 zuwa 2019 tare da karrama wasu fitattaun mutane da ke ba harkar ilimi gudummowa a yankin.
Da yake jawabi a wajen taron bikin, Hakimin dambatta kuma Sarkin Ban Kano Alhaji Muktar Adnan wanda ya sami wakilcin sakatarensa Alhaji Ado Mukhtar ya yi kira ga ‘ya’yan kungiyar da su mayar da hankali ga karatunsu tare da zama wakilan yankin na dambatta a duk inda suka sami kansu.
Har ila yau Hakimin ya yi kira ga iyaye da su zama masu bibiyar sha’anin karatu da abubuwan da ‘ya’yansu ke gudanarwa ta hanyar bayar da shawarwari tare da karafafa musu gwiwa a duk abin da suka sanya gaba, kasanacewar su ne manyan gobe.
Sabbin shugabannin da aka zaba sun hada da Hassan Musa Umar a matsayin shugaba da Maryam Musa Mukhtar a matsayin Mataimakiyar shugaba (I) sai Bashir Muhammad a matsayin Mataimakin shugaba (II). Haka kuma an zabi Usman Mahadi a matsyain sakatare. Sai Nasiru Maidaji a matsayin mataimakin sakatare. Yayin da Abba Abdula’aziz ke matsayin ma’aji, shi
kuma Asad Hamisu Ali zai rike mukamin sakataren harkokin kudi. Sai Mus’ab Umar wanda aka zaba a matsayin jami’in hulda da jama’ da Usman Shehu Abubakar a matsayin mai kula da walwalar ‘ya’yan kungiya. Har ila yau an zabi Najid Ali Baba a matsayin mai binciken kudi.
A jawabinsa sabon shugaban kungiyar Hassan Musa Umar ya yi alkawarin yin tafiya tare da kowa wajen tafiyar da harkokin kungiya don ciyar da ita gaba.
Mutanen da aka karrama wadanda kungiyar ta ce ta karrama su ne saboda irin gudummowar da suke bayarwa wajen ciyar da harkar ilimi gaba a yankin sun hada da Hakimin dambatta Alhaji Dokta Mukhtar Adnan (OFR) da Dokta Haruna Musa dankasim (BUK) da Dokta Murtala Musa dambatta (KUST) da sauransu.