kungiyar Daraktocin Jihar Kaduna ta shirya wa Shugabanta bikin ajo

A ranar Asabar da ta gabata ne kungiyar Daraktocin fina-finan Hausa reshen Jihar Kaduna ta shirya wa shugabanta Sale M Sani (Yabanya) bikin ajo, wanda ya gudana a dandalin shakatawa na Gamji da ke garin Kaduna.Bikin wanda kungiyar ta yi wa lakabi da sunan ‘Tallafi’ ya samu halartar mutane kamar su Alhaji Ibrahim Musa Gashash […]

kungiyar Daraktocin Jihar Kaduna ta shirya wa Shugabanta bikin ajo

A ranar Asabar da ta gabata ne kungiyar Daraktocin fina-finan Hausa reshen Jihar Kaduna ta shirya wa shugabanta Sale M Sani (Yabanya) bikin ajo, wanda ya gudana a dandalin shakatawa na Gamji da ke garin Kaduna.
Bikin wanda kungiyar ta yi wa lakabi da sunan ‘Tallafi’ ya samu halartar mutane kamar su Alhaji Ibrahim Musa Gashash da  fitattun ‘yan wasan fina-finan Hausa kamar su Rabi’u Ibrahim (Daushe) da Ibrahim Isa (Yado) da Hakilu Muhammad (Baban Mulika) da Alhaji Tandu da kuma Sani dan Gwari da sauransu. Hakazalika mawakan fina-finan Hausa ma, ba a bar su a baya ba, domin Sadi Sidi Sharifai da Sa’adu Gobinda sun samu halarta.
Duk da cewa bikin ba shi ne karo na farko ba amma ya kayatar da dimbin jama’ar da suka halarta. An kwashe lokaci ana cashewa da kade-kade da wake-wake iri daban-daban daga mawaka da dama, daga nan ne bikin ya kawo karshe bayan an mika kudin da aka samu ga wanda aka shirya wa bikin, inda kuma ya yi godiya ga jama’a da suka nuna masa kauna. Ya yi kuma fatan Allah Ya saka musu  da alheri.
dan wasan barkwancin nan Rabi’u Ibrahim (Daushe) ya ce bikin na da amfani matuka ba ta fuskar tallafin kudi kawai ba, saboda yadda yake kara hada kan ‘yan wasan Hausa wuri guda, wanda hakan na kara dankon zumunci da kauna da kuma fahimtar juna a tsakanin ‘yan wasa da sauran ma’aikatan masana’antar fina-finan Hausa.
kungiyar ta ce bikin tallafin zai ci gaba da zuwa duk bayan makonni biyu don nishadantar da jama’a a lokaci daya kuma don tallafa wa ‘yan kungiyar da kuma taimakawa wurin hada kan mambobinta.