Kungiyar dilallen shanu ta yi sabon shugaba a Legas

Kungiyar dilallen shanu matasa ta kasuwar shanun Abbatuwa Legas ta yi sabon shugaba bayan da ta yi zabe a karshen shekarar da ta gababta, zaben da ya gudana a tsakanin Alhaji Muhammed Tom da abokin karawarsa, Alhaji Ali Bagudo, inda Alhaji Muhammadu Tom ya yi nasarar lashe zaben bayan ya tashi da kuri’u masu rinjaye.Sarkin […]

Kungiyar dilallen shanu ta yi sabon shugaba a Legas
Kungiyar dilallen shanu ta yi sabon shugaba a Legas

Kungiyar dilallen shanu matasa ta kasuwar shanun Abbatuwa Legas ta yi sabon shugaba bayan da ta yi zabe a karshen shekarar da ta gababta, zaben da ya gudana a tsakanin Alhaji Muhammed Tom da abokin karawarsa, Alhaji Ali Bagudo, inda Alhaji Muhammadu Tom ya yi nasarar lashe zaben bayan ya tashi da kuri’u masu rinjaye.
Sarkin Fulanin kasuwar Abbatuwa, Alhaji Bello danmubaffa, wanda shi ne ya rantsar da sabon shugaban kungiyar a karshen makon da ya gabata, ya gargade shi da ya sani shugabanci riga ce ta kaya; duk inda ya juya sai ta soke shi. Don haka dole ne ya yi hakuri da jama’a, ya kuma nemi goyon bayansu a harkokinsa na shugabanci; domin a cewarsa, kasuwar shanun ta Abbatuwa kasuwa ce da ta hada kabilu daban-daban.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyyati Allah reshen Jihar Legas, Alhaji Abdullahi Lailaga, tsokaci ya yi bisa irin hadin kai da dankon zumuncin da ke tsakanin kabilun kasuwar, domin a cewarsa Fulani ne suka fi yawa a kungiyar amma sai ga shi ba tare da nuna bambanci ba sun zabi Babarbare ya shugabance su, maimakon daya dan takarar da yake Nafulatani. Ya ce wannan alamun hadin kai ne na jama’ar kasuwar. Kana ya yi fatan Allah Ya yi wa sabon shugaban kungiyar jagoranci a harkokin shugabancin jama’a.
Sabon shugaban kungiyar matasan dillallen shanun Alhaji Muhammadu Tom ya sha alwashin yin aiki tukuru domin ingantuwar rayuwar matasan kasuwar, ya kuma ba da tabbacin cewa zai yi aiki tare da abokin takararsa don cin ma nasara a jagorancin da zai yi. Ya kuma shaida cewa za su kara samar da guraban ayyukakan yi ga matasa a kasuwar, domin a cewarsa ko a yanzu akwai dimbin matasan da ke yin ayyukan dogaro da kai a kasuwar shanun ta Legas.