kungiyar dillalan man fetur a Gombe ta nada shugabannin riko
kungiyar Dillalan Man Fetur ta kasa (IPMAN), reshen Jihar Gombe ta nada shugabannin rikon kwarya da za su jagoranci kungiyar na tsawon watanni uku kafin a gudanar da zabe.Nada shugabannin rikon kwaryar ya biyo bayan rushe tsofaffin shugabanin ne da kotu ta yi a makon jiya, sakamakon dadewa da suka yi a kan karagar mulki […]
kungiyar Dillalan Man Fetur ta kasa (IPMAN), reshen Jihar Gombe ta nada shugabannin rikon kwarya da za su jagoranci kungiyar na tsawon watanni uku kafin a gudanar da zabe.
Nada shugabannin rikon kwaryar ya biyo bayan rushe tsofaffin shugabanin ne da kotu ta yi a makon jiya, sakamakon dadewa da suka yi a kan karagar mulki suka ki yarda su sauka a gudanar da zabe.
Sababbin shugabannin rikon kwaryar sun karbi kalmar rantsuwar kama aiki ne daga bakin Barista Aliyu Usman Barde, a ofishin kungiyar da ke kusa da daffon man fetur.
Alhaji Isa Muhammad JBC shi ne sabon shugaban rikon kwaryar kungiyar ta IPMAN, inda jim kadan bayan rantsar da su cikin jawabinsa na godiya, ya yi alkawarin zai rungumi kowa don ganin sun ciyar da kungiyar tasu gaba.
Alhaji Isa JBC ya ce a baya kungiyar tasu ta kusa rushewa saboda irin mulkin kama-karya da tsofaffin shugabanin nasu suka dinga yi, saboda haka ya yi alkawarin canja tsarin komai ta yadda zai tafi daidai da bukatun ’ya’yan kungiyar da sauran jama’ar da take hulda da su.
A cewarsa, wannan hobbasa da suka yi ta ceto kungiyar shi ne ya kawo har kotu ta rushe tsofaffin shugabanin saboda rashin adalcinsu, sannan kuma ya kara da cewar za su yi kokari wajen ganin sun farfado da daffon mai na Gombe.
Daga nan sai ya gode wa daukacin mambobinsu bisa hadin kai da goyon bayan da suka nuna masa inda ya kuma kara rokonsu da su ci gaba da ba shi shawarin da suka dace don ya samu damar gudanar da mulkinsa cikin adalci.
Taron ya samu halartar shugabannin kungiyar mamallaka motocin sufuri na dakon kaya ta NARTO da ta direbobin motar daukar man fetur (PTD) da shugabannin daffon mai na Gombe.
Sauran wadanda aka nada sun hada da Alhaji Abubakar Isma’il, mataimakin shugaba; Alhaji Abdullahi Mohammad, sakatare da Alhaji Sani Bagzumta, mataimakinsa; Alhaji Ahmed A. A. Garba, ma’aji; Alhaji Ahmed Makko, mai bincike; da Alhaji Inusa Gerengi, sakataren kudi.
Sai kuma Alhaji Musa Gidado, PRO; da Alhaji Nasir Habu, mai ba da shawara kan harkar shari’a, sai dattijon kungiya, Alhaji Bukar Yamele.