kungiyar direbobi a Jihar Nasarawa ta samu daukaka – Kwamared Hamza
kungiyar Direbobin gwamnati ta Jihar Nasarawa ta ce mambobinta sun samu ci gaba da kuma daukaka a karkashin gwamnatin jihar. Shugaban kungiyar Kwamared Hamza Mohammed ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu game da harkokin kungiyar a Lafiya a makon jiya.Ya ce tun da Gwamna Umaru Tanko Almakura ya karbi ragamar […]
kungiyar Direbobin gwamnati ta Jihar Nasarawa ta ce mambobinta sun samu ci gaba da kuma daukaka a karkashin gwamnatin jihar.
Shugaban kungiyar Kwamared Hamza Mohammed ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu game da harkokin kungiyar a Lafiya a makon jiya.
Ya ce tun da Gwamna Umaru Tanko Almakura ya karbi ragamar mulkin jihar direbobin gwamnati suka samu ’yanci da kuma ci gaba, sannan aka daukaka matsayinsu.
“Gwamna Almakura bai yi wata-wata ba ya mayar da direbobin gwamnati masu yawa wadanda aka sallame su ba gaira ba dalili a lokacin gwamnatocin PDP, sannan ya saya musu sabbin motoci.” Inji shi.
Ya ce wadanda al’amarin ya shafa sun wahala sosai kafin Almakura ya mayar da su wurin aikinsu, ya kuma kara musu albashi da alawus-alawus.
Ya bukaci ’yan kungiyar su rika gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da rikon amana.