kungiyar direbobi ta kama dillalin miyagun kwayoyi a Katsina

kungiyar direbobi ta NARTO a Katsina ta cabke wani dillalin miyagun kwayoyi da ya kware da amfani da motocin haya a sana’arsa. Maitaimakin shugaba na daya na kungiyar, Alhaji Ahmad Hamza ya shaida wa Aminiya cewa wani direbansu mai suna Sagir Kero ya shiga hannun jami’an hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) a Zariya. […]

kungiyar direbobi ta kama dillalin miyagun kwayoyi a Katsina

 Alhaji Ahmad Hamzakungiyar direbobi ta NARTO a Katsina ta cabke wani dillalin miyagun kwayoyi da ya kware da amfani da motocin haya a sana’arsa.
Maitaimakin shugaba na daya na kungiyar, Alhaji Ahmad Hamza ya shaida wa Aminiya cewa wani direbansu mai suna Sagir Kero ya shiga hannun jami’an hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) a Zariya. An tsare shi ne sanadiyar wani kwali mai dauke da haramtattun kwayoyi, wanda aka ba da sako a kai Katsina daga tashar motar Kawo Kaduna, amma bai san wanda ya bayar da sakon ba, balle abin da ke ciki, sai dai lambar waya da sunan wani mutum dan kabilar Ibo da ake kira Obi, wanda ke zaune a Jibiya.
Kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin kungiyar da jami’an tsaro ta sa suka shirya yadda suka kama mayaudarin boyen. “Mun shirya wata tawaga ta musamman daga cikin jami’anmu karkashin jagorancin mai kula da koke-koke tare da taimakon direba na biyu, mai suna Tsoho, wanda shi Obi ya turo daga Jibiya don daukar kayan. Shi Tsoho yakan yi wa Obi dakon kankara daga Katsina, wadda ya yi suna kanta a Jibiya, tare da kayan gini. An yi amfani da waya don sanar da Obi cewa Tsoho ya dauko kaya, amma ya sami matsala a garin Magama bayan ya je kauyen Hirji da ke kan iyaka da Nijar don kai fasinja. Obi ya shaida wa Tsoho ya jira shi a wurin ba sai ya shiga Jibiya ba, domin akwai mai kayan don wucewa da su a cikin Nijar, wasu kuma za a kai su wasu wuraren. Sai kuwa ga shi ya zo a kan babur tare da wata yarinya, wadda ita ce ke jiran kayan don shiga da su wannan kauye na Hirji da ke cikin jamhuriyar Nijar”. Inji shi.
Jami’an kungiyar ta NARTO sun kama Obi suka mika wa jami’an ’yan sanda, wadanda su kuma za su mika su inda ya dace bayan sun kammala bincike.
Dangane da direbobi, mataimakin shugaban ya yi kira gare su da yin hattara kan karbar sakon da ba su hakkake da sahihancinsa ba. Ya ce lallai duk sakon da direba zai amsa, ya tabbatar ya samu sanin wanda ya bayar da wanda za a ba, bayan samun cikakken adireshi da lambobin waya daga kowane sashe.
Haka nan ya yi kira ga fasinjoji da su rika sanar da direba ko jami’an kungiya ko na tsaro a kan duk wani abin da suke da shakku kansa da kuma kaurace wa shiga motar haya a wajen tasha, a inda ke da tashar ko wani wurin da aka kebe don amfani da shi a matsayin tasha, domin kauce wa shiga tarko ko saukin samun bacewar kayan fasinja.