kungiyar Direbobi za ta rufe tashosin da ba sa bisa ka’ida a Jihar Kebbi

kungiyar Direbobi ta kasa (NURTW) reshen Jihar Kebbi za ta rufe tashohin da ba a yi su a kan ka’ida ba.Shugaban kungiyar na jihar Alhaji Garba Kindi Koko ne ya bayyana haka ga manema labarai a lokacin da yake zagaya kananan hukumomin jihar 21, domin jin koke-koken mambobin kungiyar da kuma gane wa idonsa yadda […]

kungiyar Direbobi za ta rufe tashosin da ba sa bisa ka’ida a Jihar Kebbi
kungiyar Direbobi za ta rufe tashosin da ba sa bisa ka’ida a Jihar Kebbi

kungiyar Direbobi ta kasa (NURTW) reshen Jihar Kebbi za ta rufe tashohin da ba a yi su a kan ka’ida ba.
Shugaban kungiyar na jihar Alhaji Garba Kindi Koko ne ya bayyana haka ga manema labarai a lokacin da yake zagaya kananan hukumomin jihar 21, domin jin koke-koken mambobin kungiyar da kuma gane wa idonsa yadda sha’anin sufuri yake gudana a fadin jihar.
Shugaban ya ci gaba da cewa duk tashar motar da ba a bude ta a kan ka’ida ba za su rufe ta, domin idan aka lura da irin halin da Najeriya ke ciki na rashin tsaro dole ne kungiyarsu ta san tashoshin da aka bude a kan ka’ida domin a san direbobin da ke daukar jama’a, a san su wane ne ke shiga mota domin kauce wa duk wata ta’asa da za a taimaka a cikin al’umma.
Alhaji Garba Kindi Koko, ya ce “a kullum muna yin gargadi kan tukin ganganci da wadansu direbobi suke yi a jihar, kuma ya zama wajibi a gare mu mu ci gaba da fadakar da jama’armu domin kare lafiyar jama’a da dukiyoyinsu,” inji shi.
Shugaban ya yaba wa hukumar kare haddura ta jihar a kan yadda take ba kungiyarsu goyon baya da kuma tsawatawa ga masu tukin ganganci da kuma masu yin waya a lokacin da suke tuki, ya ce su ma fasinjoji akwai gudunmawar da za su ba da wajen hana daukar fasinjojin da suka wuce kima ko hana direbobi yin waya lokacin da suke tuki.