kungiyar direbobin gwamnati a Jihar Nasarawa ta zabi shugabanninta

kungiyar direbobin gwamnati reshen Jihar Nasarawa ta gudanar da zabe a garin Lafiya, inda Alhaji Hamza Muhammed ya zama shugaba da Ali Kigbu mataimakinsa. Alhaji Yahuza Muhammed, ya zama sakatare da Yakubu Ombugadu, mataimakinsa; Ismaila Onna, shi ya zama sakataren kudi da Ibrahim Ango, wanda ya zama ma’aji; da Steben Malle, shi ne jami’in hulda […]

kungiyar direbobin gwamnati a Jihar Nasarawa ta zabi shugabanninta

Alhaji Hamza Muhammed, sabon shugabakungiyar direbobin gwamnati reshen Jihar Nasarawa ta gudanar da zabe a garin Lafiya, inda Alhaji Hamza Muhammed ya zama shugaba da Ali Kigbu mataimakinsa. Alhaji Yahuza Muhammed, ya zama sakatare da Yakubu Ombugadu, mataimakinsa; Ismaila Onna, shi ya zama sakataren kudi da Ibrahim Ango, wanda ya zama ma’aji; da Steben Malle, shi ne jami’in hulda da jama’a (PRO); da Alhaji Inusa Adamu, darakta da kuma Alhaji Suleiman Baba Iya, Odita.
Da yake jawabi, jim kadan bayan an rantsar da su, shugaban kungiyar Alhaji Hamza Muhammed ya yi alkawarin ba za su ba wa ’yan kungiya kunya ba, saboda za su yi aiki yadda ya dace don samun cigaba mai dorewa ga kungiyar. Daga nan sai ya nemi hadin kan ’yan kungiyar don ba shi damar kai su tudun mun-tsira.
Ya kuma yi kira ga wadanda ba su yi nasara a zaben ba su dubi kaddara su zo a hada hannu tare a yi aiki don cigaban kungiyar.
Bikin dai ya sami halarcin jami’an gwamnati da jami’an tsaro, wadanda suka sa ido a kan zaben. Haka nan da shugabannin kungiyoyi daban-daban na jihar, wadanda suka hada da kungiyar kare hadurra da ta direbobin Tipa da ta direbobi masu zaman kansu, wadanda suka yi fatan alheri ga sababbin shugabannin kuma suka bukace su da su yi aikinsu kan gaskiya da rikon amana.