kungiyar Direbobin tanka ta shirya wa direbobi horo a Jos
kungiyar Direbobin Tanka ta kasa (PTD) shiyyar Kaduna ta shiryawa direbobin tanka taron kara wa juna sani kan ka’idojin tuki a kan hanyoyin kasar nan, a garin Jos fadar gwamnatin Jihar Filato.Da yake jawabi a wajen taron mataimakin shugaban kungiyar ma’aikatan man fetur ta Najeriya (NUPENG) Alhaji Tijjani Zubairu ya yi kira ga direbobin tanka, […]
kungiyar Direbobin Tanka ta kasa (PTD) shiyyar Kaduna ta shiryawa direbobin tanka taron kara wa juna sani kan ka’idojin tuki a kan hanyoyin kasar nan, a garin Jos fadar gwamnatin Jihar Filato.
Da yake jawabi a wajen taron mataimakin shugaban kungiyar ma’aikatan man fetur ta Najeriya (NUPENG) Alhaji Tijjani Zubairu ya yi kira ga direbobin tanka, su guji wasa da rayukansu ta hanyar tukin ganganci a lokacin da suke tafiya, kan hanyoyin kasar nan.
Ya ce “direbobi tun da Allah Ya ajiye abincinku a wannan sana’a don haka ya kamata ku tashi ku rike wannan sana’a hannu biyu-biyu, ku daina wasa da rayukanku.
Duk wanda yake tare da direba idan direba ya tashi kama hanya, hankalinsa ba a kwance yake ba, har sai ya dawo. Don haka bai kamata direbobin su rika wasa da rayukansu ba.”
A nasa jawabin kwamandan hukumar kiyaye hadarurruka ta Jihar Filato Crowford Oti kira ya yi ga direbobi kan su guji karya dokokin hanya.
Ya ce direbobi suna aikata abubuwa da dama da suka saba wa harkokin tuki a Najeriya.
Kwamandan wanda jami’in hulda da jama’a na hukumar a Jihar Filato AG Baza ya wakilta, ya yi bayanin cewa karya dokokin hanya ta hanyar gudu da ababen hawa fiye da kima, shi ne yake kawo yawan hadura a kasar nan.
“‘Idan muna bin dokokin hanya, sai Allah Ya kare mana hadura a kasar nan. Babu shakka yana da matukar muhimmanci direbobin manyan motoci su rika yin kokari suna bin ka’idojin tuki a Najeriya.”
Tun da farko a nasa jawabi Shugaban kungiyar Direbon Tanka ta kasa (PTD) na shiyyar Kaduna Alhaji Abubakar Njiddo ya bayyana cewa sun shirya wannan taro ne, domin su ilmantar da direbobin motocin tanka kan abubuwan da suka shafi tukin mota da ya kamata direbobin tanka su sani. Don a rage gangancin da ake yi wanda yake kawo yawan hadaru a kan hanyoyin kasar nan.
Ya ce sun zabo direbobin tanka 50 ne daga shiyoyin Jos da Yola da Gombe da kuma Maiduguri, don halartar wannan taro.
Har’ila yau, ya ce a wannan taro sun dauko jami’an hukumar kiyaye hadarurruka ta kasa da jami’an bIO da jami’an kashe gobara da likitoci don wayar da kan direbobin.
A karshe ya yi kira ga direbobin da suka halarci taron, su je su fadakar da wadanda ba su samu damar zuwa ba.