Kungiyar Direbobin Tanka za ta  taimaka wajen wadata kasa da man fetur-Tijjani Zubairu

Uban  Kungiyar Direbobin Tanka ta Kasa [PTD]  Alhaji Tijjani Zubairu ya ce kungiyar za ta  taimaka wa kamfanin mai na kasa (NNPC), wajen ganin an wadata kasar nan da man fetur a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara masu zuwa da  lokacin da za a gudanar da zabubbukan kasar nan, na shekara ta 2019. Alhaji […]

Kungiyar Direbobin Tanka za ta  taimaka wajen wadata kasa da man fetur-Tijjani Zubairu
Kungiyar Direbobin Tanka za ta  taimaka wajen wadata kasa da man fetur-Tijjani Zubairu

Uban  Kungiyar Direbobin Tanka ta Kasa [PTD]  Alhaji Tijjani Zubairu ya ce kungiyar za ta  taimaka wa kamfanin mai na kasa (NNPC), wajen ganin an wadata kasar nan da man fetur a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara masu zuwa da  lokacin da za a gudanar da zabubbukan kasar nan, na shekara ta 2019.

Alhaji Tijjani Yusuf ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi, a wajen taron kungiyar na wata uku da kaddamar da shugabannin kungiyar na shiyyar Jos, da aka gudanar a karshen makon jiya.

Ya ce sun shirya wannan taro ne domin su tattatauna hanyoyin da za su ga an wadatar da man fetur a bukukuwan sabubawr shekara mai zuwa da kuma lokacin zabubbuka masu zuwa.

Ya ce za su tabbatar an samar da wadatatcen man fetur a kasar nan. Don haka sun umarci dukan shugabannin kungiyar na dukan shiyyoyin kasar nan su tabbatar an samar da wadatattacen mai a ko’ina a  kasar nan.

‘’Kamfanin mai na kasa ya tabbatar da cewa a shirye yake wajen bai wa ’ya’yan  kungiyar goyon baya, ta hanyar samar da wadatattacen mai a kasar nan. Domin sun ce suna da mai da zai wadatar da kasar nan. Don haka muna kira ga dukan ’ya’yan kungiyar su bai wa Kamfanin NNPC goyon baya da hadin kai, don samar da wadatatcen mai a kasar nan. Kuma muna umartar ’ya’yan wannan kungiya su ci gaba da aiki har ranakun karshen mako, don ganin ba a samu karancin mai a Najeriya ba,” inji shi.

A jawabin Mataimakin Shugaban Kungiyar ta Kasa na Biyu kuma Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Filato Alhaji Dayyabu Yusuf Garga ya yi kira ga al’ummar kasar nan, su zauna lafiya musamman a wannan lokaci da zabubbukan shekara ta 2019 suka gabato.

Har’ila yau ya yi kira ga shugabannin kungiyar na shiyyar Jos da aka sake zaba, su ci gaba da tafiya da kowa da kowa a kungiyar.

A jawabin Shugaban Kungiyar na Shiyyar Jos da aka sake zaba, Alhaji Danlami Muhammad ya ba da tabbacin cewa yanzu suna da tankokin mai  sama da 80 dauke da man fetur a ma’adana ta Jos. Don haka ya ce  ba za a samu matsalar karancin mai ba a wannan shiyya, a lokacin bukukuwan sabuwar shekara.

Alhaji Danlami Muhammad ya yi bayanin cewa babban burinsa shi ne ya ga ya hada kan ’ya’yan kungiyar. Don haka ya yi kira ga ’ya’yan kungiyar su ci gaba da ba shi goyon baya da hadin kai, domin ya cimma wannan buri nasa.