kungiyar Fatu da kiraga ta zabi sabbin shugabanni

Ranar Asabar da ta gabata ne kungiyar Fatu da kiraga  reshen Jihar Kano ta gudanar da zaben shugabanninta wadanda za su ja ragamar shugabancinta na tsawon shekaru biyu. An zabi Alhaji Yahaya Gambo Lajawa a matsayin shugaban kungiyar. Har ila yau, an zabi Alhaji Tijjani dankwara a matsayinmataimaki na farko. Sai  Habibu Inuwa Sese a […]

kungiyar Fatu da kiraga ta zabi sabbin shugabanni
kungiyar Fatu da kiraga ta zabi sabbin shugabanni

Ranar Asabar da ta gabata ne kungiyar Fatu da kiraga  reshen Jihar Kano ta gudanar da zaben shugabanninta wadanda za su ja ragamar shugabancinta na tsawon shekaru biyu.
An zabi Alhaji Yahaya Gambo Lajawa a matsayin shugaban kungiyar. Har ila yau, an zabi Alhaji Tijjani dankwara a matsayinmataimaki na farko. Sai  Habibu Inuwa Sese a matsayin mataimaki na biyu.
Hakazalika, an zabi Jamiu Abdullahi Nano a matsayin sakatare Janar da Nura Isah Nalungu a matsayin mataimakin sakatare da Alhaji Aliyu Iliyasu Gaye a matsayin sakataren kudi. Yayin da aka zabi Alhaji Liti Muhamamd Officer a matsayin Ma’aji  haka kuma an zabi Alhaji Muhammad Gano a matsayin mai binciken kudi.
Sauran shugabannin sun hada da Adamu Garba Coch a matsayin jami’in hulda da jama’a da Alhaji Shehu Kano a matsayin  mashawarci harkar shari’a.
Alhaji Ahmad danliti Arzai shi ne Shugaban Kwamitin gudanar da zabe ya bayyana cewa sun samu nasarar  gudanar da zaben lafiya.
“Muna kira ga wadanda suka samu nasara da su san cewa Allah ne Ya nufa su zama shugabanni don haka su ji tsoron Allah wajen tafiyar da shugabancin. Haka su ma wadanda ba su samu nasara ba, muna kira gare su da su karbi hakan a matsayin kaddara,” inji shi.
Har ila yau, Alhaji danliti Arzai ya bayyana rashin tsaro da kasa ke fama da shi da kuma yanayin halin da kasuwa ta shiga ya matsyain abubuwan da suka janyo aka dauki tsawon shekaru ba tare da an gudanar da zaben shugabannin kungiyar ba.
A karshe sabon zababben shugaban kungiyar Alhaji Yahaya ya mika godiyarsa ga ’ya’yan kungiyar da suka dora shi a kan wannan mukami, sannan ya yi alkawarin jan ragamar kungiyar cikin adalci.