kungiyar FEDACA ta bukaci agajin gwamnati

kungiyar tsofaffin dalibai na makarantar sakandiren Gwamnatin Tarayya da ke garin Suleja a Jihar Neja, wacce a takaice ake kira, (FEDACAD), ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kaiwa makarantarsu dauki don dawo da martabar makarantar a idon jama’a. Shugaban kungiyar, reshen birnin tarayya Abuja, Faruok Muhammed Illo shi ne ya yi kiran lokacin […]

kungiyar FEDACA ta bukaci agajin gwamnati
kungiyar FEDACA ta bukaci agajin gwamnati

kungiyar tsofaffin dalibai na makarantar sakandiren Gwamnatin Tarayya da ke garin Suleja a Jihar Neja, wacce a takaice ake kira, (FEDACAD), ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kaiwa makarantarsu dauki don dawo da martabar makarantar a idon jama’a.

Shugaban kungiyar, reshen birnin tarayya Abuja, Faruok Muhammed Illo shi ne ya yi kiran lokacin da yake tattaunawa da Aminiya jim kadan bayan kungiyar ta kammala taro da manema labarai a kan bikin cikar makarantar shekaru 25 da kafuwa da kungiyar za ta gudanar kwanannan.
Ya ce, gaskiya makarantarmu ta shiga wani hali kuma abubuwa sai kara tabarbarewa suke yi.
Ya ci gaba da cewa makarantar ba ta da isassun ajujuwa da ruwan sha da wutar lantarki da isassun malamai da kuma isassun magunguna a asibitin makarantar.
“Ina so na yi amfani da wannan dama na yi kira ga gwamnati ta kawo wa makarantarmu dauki don gyara abubuwa masu yawa da suka lalace a makarantar. A yanzu makarantar tana fuskantar matsaloli da kalubale masu yawa. Kai hatta kudin da za a gudanar da makarantar babu,” inji shi.
Ya bayyana cewa babbar matsalar da take ci musu tuwo a kwarya shi ne na kudin da daliban makarantar suke biya.
Daga nan sai ya ci gaba da cewa a lokacinsu dalibi naira dari biyar suke biya, amma yanzu kudin ya fi haka.
Ya ce, duk da kokarin da kungiyar tsofaffin daliban suke yi na gyara ajujuwa da gina sabbi da samar da magunguna da ruwan sha amma duk da haka ba sa isa.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dawo da yin amfani da kundin tsarin da aka kafa makarantar na daukar dalibai masu kwazo daga kowace jiha bisa ka’ida.
“Muna so gwamnati ta tabbatar ana bin ka’idar da aka kafa makarantar na daukan dalibai bisa kwazo daga kowace jiha, amma yanzu abin ba haka yake ba sai ka ga ana daukar dalibai yadda aka ga dama,” inji shi.