kungiyar FOMWAN reshen Jihar Nasarawa ta yi sabuwar shugaba
A ranar Talatar da ta gabata ne kungiyar Mata Musulmi wato (FOMWAN) reshen Jihar Nasarawa ta samu sabuwar shugaba, inda aka nada Hajiya Rakiya Jibrin Ali. A lokacin ganawa da Aminiya bayan rantsar da ita, ta yi karin haske game da harkokin kungiyar da kuma shirye-shiryen kungiyar inda, ta bayyana cewa babban aikin kungiyar shi […]
A ranar Talatar da ta gabata ne kungiyar Mata Musulmi wato (FOMWAN) reshen Jihar Nasarawa ta samu sabuwar shugaba, inda aka nada Hajiya Rakiya Jibrin Ali.
A lokacin ganawa da Aminiya bayan rantsar da ita, ta yi karin haske game da harkokin kungiyar da kuma shirye-shiryen kungiyar inda, ta bayyana cewa babban aikin kungiyar shi ne “wayar da kawunan matan Musulmi a jihar musamman dangane da mahimmancin ilimin addini da na zamani a rayuwansu.”
Har ila yau, shugabar ta ce kungiyar tana taimaka wa mata da suka rasa mazajensu da marayu da fursunoni da kuma sauran marasa galihu a cikin al’umma da kuma gudanar da tafsir a watan Ramadan da dai sauransu.
Dangane da yadda za ta jagoranci kungiyar, ta bayyana cewa za ta ci gaba da kyawawan ayyuka da a cewarta tsohuwar shugabar kungiyar ta faro musamman na hada hannu da gwamnatin jihar wajen kwato wa matan Musulmi ’yancinsu.
Daga nan ta kara da cewa daga cikin shirye-shiryen da kungiyar za ta yi iya kokarinta wajen tabbatar da kammala ginin babbar sakatariyar kungiyar da ke garin Lafiya da kuma “tabbatar da cewa mata Musulmi a jihar sun samu ilimin addini da na zamani don tabbatar da kyawawan tarbiya a tsakaninsu da ‘ya’yansu baki daya,” inji ta.
Hakazalika, ta gode wa mambobin kungiyar a jihar baki daya da suka fito “kwansu da kwarkwata suka zabeta don ba ta damar shugabancesu”, inji ta. Har ila yau, sabuwar shugabar ta yi alkawarin cewa ba za ta ba su kunya ba. Ta kuma bukacesu su ba ta cikakken goyon ba ya don ta samu damar gudanar da shugabanci nagari.
Hajiya Rakiya Jibrin Ali dai kafin a zabenta a matsayin sabuwar shugaban kungiyar ita ce mukaddashin shugaba, inda ta gaji tsohuwar shugabar kungiyar, Barista Hannatu Muhammed bayan wa’adinta ya kare.