kungiyar FOMWAN ta yi taron wa’azi a Damaturu

kungiyar Mata Musulmi ta kasa (FOMWAN) reshen Jihar Yobe ta gudanar taron wa’azi don fadakar da mambobinta  dangane da zamantakewar zaman aure a matsayinsu na iyayengiji kuma kashin bayan tarbiyyantar da al’umma. kungiyar ta gudanar da taron ne a babbar cibiyar kula da addinin Musulunci da ke garin Damaturu.Da yake gabatar da wa’azi a wajen […]

kungiyar FOMWAN ta yi taron wa’azi a Damaturu
kungiyar FOMWAN ta yi taron wa’azi a Damaturu

kungiyar Mata Musulmi ta kasa (FOMWAN) reshen Jihar Yobe ta gudanar taron wa’azi don fadakar da mambobinta  dangane da zamantakewar zaman aure a matsayinsu na iyayengiji kuma kashin bayan tarbiyyantar da al’umma. kungiyar ta gudanar da taron ne a babbar cibiyar kula da addinin Musulunci da ke garin Damaturu.
Da yake gabatar da wa’azi a wajen taron daya daga cikin malaman da kungiyar ta gayyata Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’a wa’ikamatus-sunnah reshen Jihar Yobe Malam Ibrahim Muhammad Damaturu, inda ya bukaci mambobin kungiyar da kuma duka mata da su yi la’akari da abubuwa uku dangane halin da ake ciki don tserar da kansu da kuma al’umma fadawa halaka.
Malamin ya ce, “da farko akwai bukatar iyaye mata su yi hattara da duniya musamman yadda take shagaltar da matan na barin hanyoyin Allah tare da sa su, su bijirewa zamantakewar aure don son abin duniya fiye da biyayya ga Allah (SWT).” Har ila yau, Malam Abubakar Adam shi kalubalantar iyaye mata ya yi da su dukufa wajen tarbiyyantar da ‘ya’yansu mata don dorewar zaman aurensu da mazajensu.
Malamin ya kara da cewa “babbar gatar ‘ya mace shi ne dakin mijinta, amma idan har an ba ta tarbyiyar da za ta iya tafiyar da zama da mijinta musamman ta wajen ba ta ilimin addinin Musulunci.”  
Da take jawabi bayan kammala taron Shugabar kungiyar reshen Jihar Yobe Hajiya Halimatu Lamin Amshi bayan ta yi godiya ga malaman da suka amsa wannan gayyata da aka musu tare da ba da gudunmawarsu.