kungiyar Gamayyar jam’iyyu (IPAC) ta zabi sababbin shugabanni

kungiyar gamayyar jam’iyyun siyasa na jihar Bauchi(Inter Party Adbisory Council) ta zabi sababbin shugabanninta, wadanda za su ci gaba da jan ragamar kungiyar, har zuwa shekara daya kafin daga bisani a sake zaben wasu sabbin shugabannin. Wadanda aka zaben sun hada da Alhaji Bello Sa’idu Abubakar shugaban jam’iyyar PPN na jihar Bauchi shugaba, Alhaji Alkali […]

kungiyar Gamayyar jam’iyyu (IPAC) ta zabi sababbin shugabanni
kungiyar Gamayyar jam’iyyu (IPAC) ta zabi sababbin shugabanni

kungiyar gamayyar jam’iyyun siyasa na jihar Bauchi(Inter Party Adbisory Council) ta zabi sababbin shugabanninta, wadanda za su ci gaba da jan ragamar kungiyar, har zuwa shekara daya kafin daga bisani a sake zaben wasu sabbin shugabannin.

Wadanda aka zaben sun hada da Alhaji Bello Sa’idu Abubakar shugaban jam’iyyar PPN na jihar Bauchi shugaba, Alhaji Alkali Abdu Azare (PDM) da sakatare Honarabul Shehu Dayi (SDP) da sakataren kudi na kungiya Mahamood mai riga (AD) da ma’ajin kungiya Kwamared Muhammed dantayi(LP)Mataimakin sakataren kungiya Sai kuma aka zabi Hassan Haruna(ADC)a matsayin jami’in watsa labarai na kungiya.
Babu abin da shugabanni ke bukata a wannan lokaci kamar addu’oi da goyon baya inji Udubo
Da yake zantawa da wakilin Aminiya a ofishin hukumar zabe ta jiha (INEC), inda aka gudanar da zaben sabon shugaban kungiyar, Alhaji Bello Sa’idu Abubakar ya bayyana cewa, dukkan wadanda aka zaba shugabannin jam’iyyun siyasa ne na jihar Bauchi kuma za su ci gaba da gwagwarmaya domin ganin shugabannin da aka zaba sun cika alkawuran da suka dauka a lokacin kamfen.